Connect with us

Labarai

Dauko hayar Lauyoyi: Lauyoyin Abduljabbar sun yi suka

Published

on

Lauyan da ke jagorantar lauyoyin gwamnatin jihar Kano, Barista Surajo SAN, ya bayyana wa kotu cewar, gwamnatin jiha, ta rubuta takardun tuhuma, kuma sun roki kotun da ta janye tuhumar da ‘yan sanda su ka gabatar.

Kotun ta waiwayi lauyoyin Abduljabbar ko suna da wani jawabi kafin karanta tuhumar, inda Barrister Sale Bakaro, ya ce, “Lauyoyin da mu ka zo kotu, domin gabatar da tuhuma ba lauyoyin gwamnati ba ne saboda haka, mu na bukatar ganin takardar da aka sahale musu a matsayinsu na lauyoyi masu zaman kan su, kuma yanzu su ka zo a matsayin lauyoyin gwamnati”.

Barista Surajo ya bayyana cewar, “Ai lauya ba shi da hurumin ya tuhumi lauya a kan batun tsayawa a gaban kotu, saboda haka su bari a karanta takardar tuhuma sai su yi suka”.

Daga nan Surajo Sa’ida SAN, ya dauko takardar da Kwamishin Shari’a ya ba su, a matsayin an sahale musu su gurfanar da malamin ya mikawa kotun.

Kotun ta mikawa lauyoyin Abduljabbar takardun sahalewar, sai dai lauya Sale Bakoro ya ce, “Mu na da suka a kan takardar, domin dokar da aka dogara da ita aka ba su takardar ba ta cikin dokar kundin tsarin mulkin kasa, kuma takardar tuhumar da su ka sake kawowa, itama ta sabawa doka”.

Ya kuma ce, “Saboda haka da kwamishinan Shari’a da wadannan manyan lauyoyi, sun gaza kawowa kotu wata doka wadda za ta dogara da ita, wannan takardun zargi kamar ma babu su, domin wadannan manyan lauyoyi, su ne suka sanya hannu a kan takardar, su kuma basu da hurumin zuwa su wakilci gwamnati”.

Ya kara da cewar, “Doka bata bawa lauya mai lambar SAN, hurumin ya je kotun da ta gaza babbar kotun jiha ba, aikin lauya ya na da tsari, saboda haka doka bata yadda SAN, ya zo irin wannan kotun ba bare ma har yayi magana a saurare shi. A shari’ar muslunci ba a canza da’awa, ko ayi kari ko ragi kamar yadda su lauyoyin gwamnati su ka yi yanzu”. Inji lauya Bakoro.

Labarai

Ƙaramar hukumar Tofa ta dakatar da sayar da Burtalai a wasu garuruwan ta

Published

on

Biyo bayan kokawar da wasu Fulani Makiyaya suka yi kan yadda wasu suka gididdiba burtalai yayin da aka siyarwa Manoma, a garuruwan Yanoko da Gajida da kuma Dindere, yanzu haka ƙaramar hukumar Tofa ta dakatar da taɓawa, ko kuma sayar da dukkanin Burtalan kiwon shanun ba tare da ɓata lokaci ba.

Shugaban riƙon ƙaramar hukumar ta Tofa Abubakar Sulaiman Mai Rogo, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa Dala FM Kano, a ranar Alhamis.

Mai Rogo, ya kuma ce ƙaramar hukumar ba ta da hannu a kan taɓa dukkan guraren, a dan haka sun dakatar da dukkanin yunƙurin taɓa Burtalan har sai shugabanni na kwamitin ƙasa sun kammala bincike wanda yanzu haka ake ci gaba da yi.

Da yake nuna jin daɗin sa kan matakin dakatarwar, amadadin Fulanin garuruwan, shugaban ƙingiyar Funali Makiyaya ta Gan Allah, Ahmad Shehu Gajida, yabawa gwamnatin jihar Kano, da kuma ƙaramar hukumar ta Tofa ya yi, bisa karɓar koken su da suka akai.

A baya-bayan nan ne dai a zantawar Dala FM Kano, da wasu Funalani Makiyaya mazauna garuruwan Yanoko da Gajida da kuma Dindere, suka koka kan yadda aka gididdiba burtalan a yankunan nasu aka siyarwa manema, lamarin da suka ce ka iya sawa su rasa guraren da za suyi kiwon shanun su wanda hakan babbar barazana ce a gare su.

Continue Reading

Labarai

Ku guji zubar da Shara barkatai a muhallan ku – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi al’umma da su kaucewa zubar da shara a wuraren da ba’a tanade su ba, domin kaucewa yawaitar samun cutuka a tsakanin al’umma, duba da yadda ake ci gaba da tunkarar lokacin Damuna.

Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano Ambasada Ahmadu Haruna Zago, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake sanya ido kan aikin kwashe sharar da ke unguwar Zango hauran gadagi bayan Festival.

Ya ce duba da yadda Damuna ke ci gaba da tunkarowa, akwai bukatar al’umma su fahimci cewa zubar da shara barkatai ka iya haifar da cututtuka daban-daban ga iyalan su, musamman ma kasancewar sharar da ke unguwar ta Zango bayan Festival, tana tsakiyar gidajen al’umma ne da kasuwa da kuma makaranta.

Nazifi Mohammed Usman mai Duniya, da Mohammed Ibrahim wato Halifa mai Gas mazauna unguwar ta Zango ne, sun ce tarin sharar a cikin unguwar su babban ƙalubale ne a gare su, domin kuwa taruwar da tayi har ta kan shiga cikin makarantar yankin su.

Shugaban hukumar kwashe sharar Ahmadu Zago, ya kuma sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen tsafta ce birnin Kano, wajen kwashe shara daga kowane yankin, domin gudun faruwar ambaliyar ruwa sanadin sharar da ka toshe magunan ruwa a jihar Kano.

Continue Reading

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Trending