Addini
Rahoto: Kungiyar dalibai musulmai na bayar da bita a Kano
Kungiyar dalibai musulmai ta kasa reshen jihar Kano (MSSN), ta ce bitar wayar da kan dalibai a jihar zai bunkasa musu ilimi na gudanar da rayuwa.
Sakataren gudanar da taron, Saifullahi Yusuf Indabawa ne, ya tabbatar da hakan lokacin da dalibai musulmai na Kano ke daukar bita a makarantar mata ta GGAC Goron Dutse.
Wakilin mu na ‘yan Zazu Tijjani Adamu ya aiko mana da cikakken rahoton.
Addini
Ku taimakawa mabuƙata da Naman Sallah bisa halin matsin rayuwar da ake ciki – Limami
Babban limamin masallacin juma’a na Alaramma Abubakar Ɗan Tsakuwa, da ke unguwar Ja’en Ring road Mallam Abdulkareem Aliyu, ya yi kira ga al’ummar Musulmi, da su kiyaye ƙa’idojin yanka Dabbobin Layyah, domin gujewa cin mushen Nama.
Mallam Abdulkareem Aliyu, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u, lokacin da yake tsokacin huɗubar da ya gabatar ranar Sallar Idin da ya jagoranta a masallacin ranar Lahadi 17 ga watan Yunin 2024.
Ya ce a mafi yawan lokuta al’umma sukan yanka dabbobi amma rashin bin ƙa’idojin yanka yakan sanya wa su ci mushen nama ba tare da sun sani ba, a dan haka su tashi tsaye wajen sanin yadda ake yanka Dabbobin a mahanga ta addinin Musulunci.
A cewar sa, “Musulmai ku kwaɗaitu da yin sadakar naman layya musamman ma ga masu ƙaramin ƙarfi domin rabauta da rahamar Ubangiji S.W.T, “in ji shi”.
Mallam Abdulkareem Aliyu, ya kuma ce, akwai buƙatar a kiyaye nau’ikan dabbobin da aka sahale ayi layya da su, waɗanda suka haɗar da nau’in Sa ko Saniya, da kuma Raƙumi ko Raƙuma (Taguwar), ko kuma Rago ko Tinkiya, ko Akuya ko kuma Ɗan Akuya.
Wannan dai na zuwa ne bayan da al’ummar Musulmin Duniya suka gudanar da babbar Sallah, a jiya Lahadi 16 ga watan Yunin shekarar 2024.
Addini
An ga jinjirin watan Zul-Hijjah a Najeriya, ranar Lahadi 16 ga watan Yuni Babbar Sallah
Fadar mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Abubakar Sa’ad na uku, ta sanar da ganin jinjirin watan Zul-Hijjah na shekarar 1445.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da fadar Sarkin Musulmin ta fitar, mai ɗauke da sa hannun Wazirin Sakkwato, kuma shugaban kwamitin duban wata Farfesa Sambo Wali Junaid.
Sanarwar ta kuma ce duba da ganin jaririn watan na Zul-Hijjah da akayi a jiya Alhamis, hakan ya tabbatar da cewar yau Juma’a ɗaya ga watan Zul-Hijjah, wanda za’ayi babbar Sallah a ranar Lahadi 16 ga watan Yunin 2024.
Tun dai a jiya Alhamis hukumomi a ƙasar Saudiyya suka sanar da ganin Jaririn watan na Zul-Hijjah, lamarin da ya kasance za’ayi tsayuwar Arafa a ranar Asabar 15 ga watan Yunin 2024, yayin da za’ayi babbar Sallah a ranar Lahadi 16 ga watan na Yuni.
Kafar Dala FM Kano, ta rawaito cewa, kawo yanzu dai maniyyata aikin hajjin bana da dama ne ke ci gaba da shiga ƙasa mai tsarki, a ƙoƙarin su na zuwa domin sauke Farali.
Addini
Matsin Rayuwa: Shugabanni ku sassautawa al’umma – Babban Limamin Kano
Babban limamin Kano, kuma wanda ya jagoranci sallar idi a babban masallacin idin na Kofar Mata a nan Kano, Farfesa Muhammed Sani Zaharaddin, ya ja hankalin shugabanni da su sassautawa al’umma, sakamakon halin matsin rayuwar da ake ciki a yanzu.
Farfesa Muhammed Sani Zaharaddin, yayi jan hankalin ne yayin huɗubar da ya gabatar, bayan kammala sallar idi da ta gudana a yau Laraba, a babban masallacin idin dake unguwar Kofar Mata a Kano.
Ya kara da cewa kasancewar al’umma na cikin mawuyacin hali da kuncin rayuwa, akwai buƙatar shugabanni su yi bakin ƙoƙarin su, domin kawo sauki daga halin matsin halin rayuwar da ake fama dashi.
Yayin sallar Idin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da mataimakin sa Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da sauran al’umma da dama ne suka halarta.
Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Abba Haruna Idris ya rawaito cewa, Farfesa Muhammed Sani ya kuma ja hankalin al’umma, da su koma ga Allah Subhanahu wata’ala domin samun dacewa a Duniya da gobe Ƙiyama.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su