Connect with us

Labarai

Abincin 30: Na ji dadi da a ka sauke Nanono – Mai Kwakin 30

Published

on

Mutumin nan wanda ya siyar da Kwakin Naira 30 a jihar Kano, Alhaji Haruna Injiniya mai Kwakin 30, ya ce tabbas ya ji dadin sauke Ministan harkokin Noma Sabo Nanono daga mukamin sa.

A wata tattaunawa da Dala FM ta yi da Haruna Mai Kwakin 30, wanda a baya ya bude shagon siyar da Kwakin 30 a unguwar Sani Mainagge dake karamar hukumar Gwale a jihar Kano.

Haruna Mai Kwakin 30, ya dai bude shagon ne, a lokacin da tsohon Ministan harkokin Noma ya bayyana cewa abincin 30 zai ishi mutum ya ci ya koshi, komai ya tsefe, shikafa da mu ke siyan ta 250, 300 kwano ta koma Dubu da wani abu

Mai Kwakin 30 ya ce” Ko a yanzu kwanan Garin Kwaki ya kai Naira 900, sabanin a baya mu na siya a Naira Dari Biyu”.

A batun tsige Ministab kuwa, Haruna mai Kwakin 30 ya kuma ce,”Na ji dadin tsige Ministan harkokin Noma da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, saboda ban samu damar ganin shi ba tun a lokacin, saboda mu tattauna da shi a kan batun”. Inji Haruna Mai Kwakin 30.

ga muryar magidancin mai suna Haruna Mai Kwakin 30.

Labarai

Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya naɗa Ɗan Sa a matsayin Chiroman Kano.

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya buƙaci dukkanin hakimansa da ke faɗin jihar nan da su mayar da hankali wajen gudanar da aikin su bisa gaskiya da riƙon Amana.

Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, kuma babban ɗan fadar Sarki, yau Juma’a a fadar sa.

Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya ce ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, ne bisa cancanta da zuminci da kuma gogewarsa akan aikinsa na ƴan sanda, tare kuma da taimakawa al’umma da yake yi a koda yaushe.

Mai martaba sarkin ya kuma taya Chiroman Kano, murna bisa wannan naɗin da aka yi masa, tare da fatan zai zamo jakada na gari musamman wajen samar da cigaban Al’umma da kuma masarautar Kano.

Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa taron naɗin ya samu halartar gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da sarakunan gargajiya daga wasu daga cikin jahohin ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Za mu magance matsalolin da hukumar Hisbah ta Dala ke fuskanta – Shugaban ƙaramar hukumar Dala

Published

on

Ƙaramar hukumar Dala ta ce za ta yi bakin ƙoƙarin ta wajen magance matsalolin da hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala ke fuskanta, domin ƙara ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukan al’umma.

Shugaban ƙaramar hukumar Suraj Ibrahim Imam ne ya bayyana hakan, a lokacin da jami’an hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala, suka ziyarce shi a ofishinsa, domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da suka yi, tare da sanar dashi halin da hukumar Hisbar ke ciki a halin yanzu.

“Daga cikin ƙalubalen da zan yi ƙoƙarin magance wa akwai samar da ruwa da wutar lantarki da kuma samar wa hukumar kayan aiki, bisa yadda suke fama da rashin su, “in ji Suraj Imam”.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Dala Sura ya kuma yi kira ga babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da ya ƙara kulawa da walwalar hukumar ta ƙaramar hukumar Dala bisa ƙalubalen da suke fuskanta.

Da yake nasa jawabin kwamandan hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala Mallam Umar Bala Muhammad, ya ce sun ziyarci shugaban ƙaramar hukumar ne domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da kuma sanar da shi halin da hukumar ke ciki, domin haɗa ƙari da ƙarfe wajen magance ƙalubalen da suke fuskanta.

Wakiliyarmu Hadiza Balanti ta rawaito cewa Mallam Umar Bala ya kuma ƙara da cewa a shirye hukumar hisbar ta ƙaramar hukumar Dala take wajen gudanar da ayyukan al’umma babu gajiyawa.

Continue Reading

Labarai

Mun dakatar da karɓar kuɗin haraji a Fagge har sai an kammala bincike – Shugaban Ƙaramar hukumar Fagge

Published

on

Ƙaramar hukumar Fagge ta dakatar da dukkannin harkokin karɓar haraji har zuwa lokacin da za’a kammala bincike, don tabbatar da cewa bangaren harajin nayin aiki bisa doka domin ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Fagge Salisu Usman Masu ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da tashar Dala FM Kano, a safiyar yau Talata.

Salisu Usman ya kuma bayyana cewar duk filotan da aka yanka aka sayar ko aka bayar ba bisa ƙa’ida ba shima an soki shi.

Shugaban ya kuma yi kira ga ƴan kwangila waɗanda suka watsar da ayyukan da aka basu da su dawo bakin aiki ka’in da na’in.

A cewar sa, “Na fahimci irin kalubalen da ke damun al’umma a ɓangaren lafiya a ƙaramar hukumar mu ta Fagge; kuma za mu yi ƙoƙarin samar da kayan aiki domin magance matsalar, “in ji shi”.

Masu ya kuma bayyana cewar ƙaramar hukumar ta Fagge za ta inganta harkar ilimi da tsaro, da Lafiya, inda kuma yi kira ga duk wani mai kaunar ci gaban karamar hukumar Fagge da ya taho a hada hannu ko da shawara zai bayar dan ciyar da karamar hukumar gaba.

Continue Reading

Trending