Connect with us

Wasanni

Gago Challenge Cup: Highlanders ta doke Kano Ambassadors

Published

on

A ci gaba da gasar Umar Gago Challenge Cup da ke wakana a filin wasa na Dorayi Babba Lions da ke bayan masallacin Juma’a na Dan Sarari.

kungiyar kwallon kafa ta Highlanders ta lallasa Kano Ambassadors da ci 2 da nema.

A wasan da za a fafata a yammacin Juma’a, Chiranci United za ta barje gumi da Kano Municipal a filin wasa na Dorayi Babba Lions.

Wasanni

Usman Abdullahi Zawaciki ya lashe gasar tseren keke ta Alaramma

Published

on

Ƙungiyar Tseren ce mai suna Alaramma Cycling Club ta shirya Tseren keke na dukkanin shekara shekara da ta saba haɗawa, wanda a wannan shekarar a ka haɗa wasan a safiyar ranar Lahadin da ta gabata a kan titin tsohuwar Jami’ar Bayero ta Kano, inda daga nan masu tseren su ke zagayawa ta kabuga su biyo ta Tal’udu su dawo wajen da a ka shirya haɗuwa.

Gasar dai akwai na yara sai kuma na manya, kuma bayan da a ka kammala tseren kekunan ne mu ka ji ta bakin wanda yazo na farko a ɓangaren manya, Usman Abdulmuɗallib Zawaciki, ya ce”Babban buri na shi ne na zama gwarzo a gasar tseren keken a duniya”.

Rabi’u Abdullahi shi ne shugaban ƙungiyar gasar tseren keken na jihar Kano ta Alaramma Cycling Club, ya bayyana cewar akwai kyauta ga waɗanda su ka samu nasara, kuma za su cigaba da shirya wasan ba tare da gajiyawa ba.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u, ya rawaito mana cewa, bayan kammala gasar an bawa waɗanda su ka zo na 1-2-3 kyauttuka, kuma daga ƴan ajin yara da kuma ƴan ajin manya.

Continue Reading

Wasanni

Lahadi: Za a fara gasar tseren Keke a titin BUK

Published

on

Kungiyar tseren keke ta Arramma dake Panshekara a ƙaramar hukumar Kumbotso, Za ta gudanar da gasar tseren Keke a safiyar ranar Lahadi.

Wasan za a fara shine da karfe 8 na safe a kan titin jami’ar Bayero.

Cikin wata sanarwa da shugaban shiyra gasar, Yahaya Arramma, ya tabbatar da hakan ga gidon rediyon Dala FM.

Ya ce,”Tseren keken za a bi ta Tal’udu a bi ta Gadon Ƙaya sai kuma a bi ta titin Jam’iar Bayero ta Kano (BUK). Kuma wannan shi ne karo na biyu da za mu gudanar da gasar a Kano, bayan da mu ka yin a farkon a kan titin Jafar Mahmud Adam na Dorayi”. Inji Yahaya.

Continue Reading

Wasanni

Za mu warware matsalar tsakanin gidan kallo na da magoya bayan Arsenal – Hamisu Abubakar

Published

on

Magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal a jihar Kano, ta umarci magoya bayan ƙungiyar da su ƙauracewa shiga gidan kallon ƙwallon ƙafa na unguwar Makasa da ke Ɗan Rimi a ƙaramar hukumar Gwale.
Shugaban ƙungiyar na jihar, Ibrahim London Boy ne ya tabbatar da hakan ta bakin babban sakataren ƙungiyar, Aminu So Far Mai Arsenal.

Shugabancin ya yanke wannan hukuncin ne, sakamakon zargin cin zarafin magoya bayan Arsenal da a ka yi a gidan Kallon na yin ɓangaranci.


Sanarwar ta ƙara da cewa, ƙungiyar su ta shigar da ƙara zuwa shugabancin da ke jihar Legas, wanda hakan ya ba su damar shigar da ƙorafin su zuwa ƙungiyar da ta ke kula da gidajen kallon ƙwallon ƙafa a jihar, amma kawo yanzu ba su ji amsa ba, wanda shugabancin magoya bayan ƙungiyar ya yi kira ga ƴaƴan ta da su ƙauracewa shiga gidan kallon har sai sun ji amsa a nan gaba.


Mun kuma tuntuɓi mai gidan kallon, Hamisu Abubakar, ya ce za su yi zama da shugabancin kungiyar ta Arsenal nan da mako mai zuwa, domin warware matsalar, kamar yadda su ka cimma matsaya tsakanin shugabancin da kuma shi kan sa mai gidan kallon.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!