Connect with us

Kimiya

Duk saurayin da ya zo wajen ku indai ba aure zai yi ba ku yi watsi da shi – Dr. Abdallah

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Usman Bin Affan da ke unguwar Gadoan Ƙaya, Dr. Abdullah Usman Umar ya ce, bai kamata samari su rinƙa yin watsi da shawarwarin iyaye ba, a yayin da su ke neman aure.

Dakta Abdallah Gadan Ƙaya, ya bayyana hakan ne, ta cikin shirin Rayuwa Abar Koyi, na gidan rediyon Dala FM, wanda ya gudana a ranar Juma’a.

Ya ce, “Mafi yawan lokuta, samari su kan fi neman shawarar abokan su, a yayin da su ke neman aure, mai-makon shawarar iyayen su”. A cewar Dakta Abdallah.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito Cewar, Dakta Abdullah Usman, ya kuma shawarci ‘ƴan mata, a kan duk saurayin da ya zo wajen su zance, matuƙar ya na neman ɓata musu rayuwa, to su kore shi, domin kaucewa lalata musu rayuwa.

Kimiya

Gwamnati ta samar mana da Injin lauya Robobi – Mai sana’ar Liki

Published

on

Wani matashi, Mubarak Badamasi, mai sana’ar likin robobin Babur ya ce gwamnati ta waiwayi masu kananan sana ‘oi, musamman ma irin na su ta likin roba.

Matashin na wannan bayanin ne a lokacin da ya ke ganawa da wakilin mu Nasir Khalid Abubakar.

Ya ce,” Lallai da gwamnati ta waiwayo kan mu da ta Sami kudin shiga da kuma rage rashin aikin yi a tsakanin matasan mu. Saboda da gwamnati za ta ba mu jari ko ta samar mana da injinan lauya Roba da sana’ar mu ta bunkasa”. Inji Mubarak Badamasi.

Continue Reading

Kimiya

Rahoto: Kasuwar gwanjon kayan al’umma na ci gaba da habaka a kotu

Published

on

An ci gaba da gwanjon kayayyakin wasu mutanen da kotu ta yi hukunci a kan su, saboda gaza biyan bashi a harabar kotunan Majistret na Noman’s Land.

Al’umma sun ci gaba da ziyartar harabar kotunan, domin siyen kayayyakin da a ka yi gwanjon su a ranar Laraba.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il nada cikakken rahoton.

Continue Reading

Kimiya

Covid-19: Za a gina cibiyar gwajin Corona a Jigawa

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ta na aikin gina cibiyar gwajin cutar Covid-19 da zai fara aiki nan da makonni biyu masu zuwa.

Gwamnan jihar Alh. Muhd Abubakar ne ya sanar da hakan ga manema Labarai da yammacin ranar Talata a gidan Gwamnatin jihar dake Dutse.

Gwamnan ya ce” Mun dauki wannan mataki ne sakamakon kalubalen da jihar ke fama da shi na rashin cibiyar gwaji wanda hakan ke janyo jinkirin gano masu dauke da cutar. Wannan cibiya za a yi mata matsugunni ne a wani sabon sashe dake cikin babban asibitin Dutse, wato Dutse (General Hospital)”. Inji Badaru.

Wakilin mu Muhd Aminu Umar Shuwajo ya rawaito gwamnan na cewa wannan cibiya ko da bayan cutar Coronavirus, cibiyar za ta cigaba da gwajin cututtuka irin su Ebola da Lassa da dai sauran cututtuka masu yaduwa.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!