Connect with us

Labarai

Matsalar tsaro: Sai an yi maganin masu goya wa ƴan bindiga baya – Umar Ɗan Baito

Published

on

Lauyan nan mai zaman kan sa a jihar Kano, Barista Umar Usman Ɗan Baito ya ce, matuƙar a na son a shawo kan matsalar tsaro a Najeriya, sai an yi maganin waɗanda su ke goya wa ƴan bindiga baya.

Umar Ɗan Baito ya bayyana hakan ne, ta cikin shirin Ɗaurin Ɓoye na gidan rediyon Dala FM, wanda ya gudana a karshen makon da ya gabata.

Ya ce, “Mafi yawan lokuta, rashin ɗaukar mataki ga waɗanda su ke mara wa ɓata gari baya ne, ya ke sanya wa matsalar tsaron, hakan kuma ta kan ƙara gaba maimakon daƙile ta”. A cewar Danbaito.

Da ya ke nasa jawabin ta cikin shirin mai sharshi a kan al’amuran yau da kullum, Alhaji Bello Basi Fagge, bayyana  cewar, “Matuƙar gwamnati ta na son daƙile matsalar cin hanci da rashawa a Najeriya, to kuwa  babu shakka, sai an fara daga sama”.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Barista Umar Usman Ɗan Baito ya kuma ce, kamata ya yi ƴan majalisar tarayya da na jihohi, su fi mayar da hankali ga samar da dokoki a ƙasar nan, mai-makon kawo ayyuka da a ke fakewa da su a na cin hanci da rashawa.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending