Connect with us

Wasanni

Za mu warware matsalar tsakanin gidan kallo na da magoya bayan Arsenal – Hamisu Abubakar

Published

on

Magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal a jihar Kano, ta umarci magoya bayan ƙungiyar da su ƙauracewa shiga gidan kallon ƙwallon ƙafa na unguwar Makasa da ke Ɗan Rimi a ƙaramar hukumar Gwale.
Shugaban ƙungiyar na jihar, Ibrahim London Boy ne ya tabbatar da hakan ta bakin babban sakataren ƙungiyar, Aminu So Far Mai Arsenal.

Shugabancin ya yanke wannan hukuncin ne, sakamakon zargin cin zarafin magoya bayan Arsenal da a ka yi a gidan Kallon na yin ɓangaranci.


Sanarwar ta ƙara da cewa, ƙungiyar su ta shigar da ƙara zuwa shugabancin da ke jihar Legas, wanda hakan ya ba su damar shigar da ƙorafin su zuwa ƙungiyar da ta ke kula da gidajen kallon ƙwallon ƙafa a jihar, amma kawo yanzu ba su ji amsa ba, wanda shugabancin magoya bayan ƙungiyar ya yi kira ga ƴaƴan ta da su ƙauracewa shiga gidan kallon har sai sun ji amsa a nan gaba.


Mun kuma tuntuɓi mai gidan kallon, Hamisu Abubakar, ya ce za su yi zama da shugabancin kungiyar ta Arsenal nan da mako mai zuwa, domin warware matsalar, kamar yadda su ka cimma matsaya tsakanin shugabancin da kuma shi kan sa mai gidan kallon.

Wasanni

Tofa Premier League: Kano Lions za ta barje gumi da Good Boys Dorayi

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Lions za ta barje gumi da Good Boys Dorayi a ranar Asabar da karfe 2 na ranar Asabar a filin wasa na Kofar Mata.

Dorayi United za ta kara da Dabo Feeder da karfe 2 a filin wasa na Kano Pillars da ke Sabon Gari.

Kano Municipal za ta kara da Golden Bullet da karfe 4 na yamma a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata.

Tsamiya Utd za ta buga da FC Sheshe a filin wasa na Kano Pillars da ke Sabon Gari.

Continue Reading

Wasanni

Kano Lions: Mu na mika sakon ta’aziya ga kungiyar Gwammaja United – Coach Amo

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Lions, ta mika sakon ta’aziyar ta ga mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Gwammaja United, Caoch Sagiru Sagi, bisa rasuwar Kakar sa.

Sanarwar mai dauke da jami’in hulda da jama’a na kungiyar, Injinya Abba Zubair, ta ce a madadin jagorancin shugaban kungiyar Sa’ad Ahmad Ma’aji Coach Amo, ta kuma yi addu’ar fatan shiga Aljanna tare da baiwa iyalanta baki daya hakurin juriya.

Continue Reading

Wasanni

Tofa Premier League: Masu kungiyoyi sun mika ta’aziyar su ga Rabi’u Chanhu

Published

on

Masu kungiyar kwallon kafa wanda su ke buga gasar Tofa Premier League a jihar Kano, ta mika sakon ta’aziyar ta ga mai kungiyar kwallon kafa ta Sharada United, Rabi’u Chanhu, bisa rasuwar matar sa.

Shugaban masu kungiyar Alhaji Yahaya Minister ya mika sakon ta’aziyar ne ta hannun sakataren masu kungiyoyin Tofa Premier League, Yusuf Isah Sa’ad wanda a ka fi sani da Guarantee.

Kungiyar masu kungiyoyin Tofa Premier League tare da magoya bayan su, sun kuma yi wa matar Rabi’u Chanhu fatan Allah ya sanya ta a Aljanna.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!