Labarai
Rahoto: A na zargin matasa da satar dabbobi a Adaidata

Dubun matasan ta cika ne a yankin Samegu dake karamar hukumar Kumbotso, bayan da a ka yi musu kururuwar dauki na zargin satar Awakai da Tumakai.
‘Yan Sintirin yankin Zawaciki da Gaida ne su ka samu nasarar kama matasan, bayan da su ka biyo su tun daga Zawaciki har zuwa Samegu.
Wakilin mu na ‘yan Zazu, Tijjani Adamu, ya na da cikakken rahoton.

Baba Suda
Hukumar tattara kudaden shiga ta Kano ta rufe wasu bankuna

Hukumar Tattara kudaden shiga ta jahar kano ta kulle bakin Eco da Zenith dake kan titin Murtala Muhammad. Sakamakon rashin biyan haraji.
Cikakken labarin na Zuwa….

Baba Suda
Kisan Makurdi:- Gwamnatin Kano za ta tura wakilai

Gwamnatin Jihar Kano tayi Allah wadai da kisan mutane biyu Yan Jihar a garin Makurdi dake Jihar Benue.
Cikin sanarwar da Daraktan Gwamnan Kano kan harkokin yada labarai Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ruwaito Gwamnan na Mika sakon jaje ga alummar Jihar da iyalai da ‘yan uwan wadanda abin ya rutsa dasu, Barhma Suleman da Jamilu Ahmad.
Kazalika Gwamnan yayi alkawarin daukar Matakin da ya dace kan batun, tare da fadin gwamnatin Kano za ta tashi wakilai har Zuwa Jihar Benue domin tabbatar da daukar Matakin da ya dace.

Baba Suda
NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.
Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.
A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.
Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.

-
Nishadi6 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su