Wasanni
Gwale Football Council: Wasan kusa da na karshe

Wasanni
West ham united ta lashe kofin conference

Kungiyar kwallon kafa ta West Ham United ta yi nasarar lashe gasar Europa Conference na nahiyar turai, bayan doke kungiyar kwallon kafa ta Piorentina da ci biyu da daya.
Dan wasan kungiyar West Ham Benrahma ne ya fara zura kwallo a minti na 62, daga bisani dan wasan Piorentina Benoventure ya farke kwallon a minti na 67,gab da tashi daga wasan dan wasa Bowen ya tasa West Ham a gaba a bugun daga kai sai mai tsaron raga a minti na 90, inda aka tashi kwallon kungiyar kwallon kafa ta Piorentina na da kwallo daya West Ham United na da kwallo biyu.
Tin a shekarar 1980 rabon da kungiyar kwallon kafa ta West Ham ta lashe wani kofi, shekaru 43 kenan.
West Ham dai, itace kungiya ta biyu da ta lashe gasar ta Europa Conference a tarihi, bayan kungiyar kwallon kafa ta Roma da ta fara lashe gasar a karon farko a kakar shekarar 2021 zuwa 2022.

Wasanni
Sevilla ta lashe kofin Europa na nahiyar turai

Kungiyar kwallon kafa ta Sevilla da ke kasar Spain ta lashe kofin Europa na nahiyar turai, na shekarar 2022 zuwa 2023, inda ta doke kungiyar kwallon kafa ta Roma da ke kasar Italiya da ci hudu da daya a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Tun da fari dai, kungiyoyin sun kwashe mintuna 120 suna fafatawa a tsakaninsu, daga nan ne suka tafi bugun daga kai sai mai tsaron raga, wato Penalty a turance, inda kungiyar kwallon kafa ta Sevilla ta doke kungiyar kwallon kafa ta Roma da ci hudu da daya wanda hakan ya bata damar lashe gasar, wanda shine karo na bakwai jimulla da Sevillan ta lashe.

Manyan Labarai
Babban kuskure ne Manchester City ta nemi daukan fansa a kan Madrid – Guardiola

Mai horas da kungiya kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola ya ce, kungiyar sa ta Manchester City, za ta yi babban kuskure, matukar ta yi yunkurin cewa za ta dauki fansa ne akan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, a karawar da kungiyoyin biyu za su yi a daren yau Talata a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin kungiyoyin zakarun nahiyar turai.
Guardiola, ya bayyana hakan ne a wata zantawa da yayi da manema labarai.
Inda ya kara da cewa, kamata ya yi kungiyar ta Manchester City, ta yi amfani da wannan damar wajen doke Real Madrid masu rike da gasar, hakanne kawai zai iya kai su ga wasan karshe, daga bisani kuma su yi nasarar lashe gasar.
“Abun da ya faru a baya ya riga da ya faru, darasin da muka dauka a bara ba daukan fansa bane mafita, yin aiki mai kyau shine zai kaimu ga samun sakamako mai kyau”. A cewar Guardiola.

-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano