Connect with us

Labarai

Rahoto: Giya na sha har na haike wa ‘yar shekaru 4  – Magidanci

Published

on

Wani mutum da ake zargi da haike wa karamar yarinya a garin Wudil, mai suna Nasiru Umar ya ce, giya abokan sa su ka zuba masa ya sha, ya fita hayyacin sa har wata yarinya ta shigo gidan sa diban ruwa, ya yi yunkurin haike mata.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, a zantawar sa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Abba Isah Muhammad, ya bayyana cewar, yanzu haka Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, ya bayar da umarnin dawo da shi babban sashen binciken manyan laifuka, da ke Bompai.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Labarai

Rahoto: Mu tuba ga Allah domin fita daga tsanani – Limamin Na’ibawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Nana Aisha da ke unguwar Na’ibawa Gabas, Malam Abubakar Jibril ya ce, al’umma su tuba zuwa ga Allah, domin ya musanya tsanani zuwa yanayi na walwala.

Malam Abubakar Jibril, ya bayyana hakan ne ta cikin Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke ƙasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rashin wadatar zuci ke janyo zalinta a tsakanin al’umma – Limamin CBN Quarters

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Faruq Unguwa Uku CBN Quarters, Dr. Aminu Ismai’l, ya ce, rashin wadatar zuci ke janyo zalunci da cutar wa a tsakanin al’umma.

Dr. Aminu Isma’il, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ke yi wa Dala FM ƙarin bayani dangane da Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu guji yin ƙarya da yaɗa ta – Limamin Chiranchi

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Sheikh Aliyu Harazimi da ke unguwar Chiranchi, a ƙaramar Hukumar Kumbotso, Dr Rabi’u Tijjani Rabi’u, ya ja hankalin al’ummar Musulmi da su guji yin ƙarya da kuma yaɗa ta.

Dr. Rabi’u ya bayyana hakan ne, yayin da yake ƙarin haske dangane da abin da huɗubar sa ta ƙunsa.

Wakilin mu na ƴan Zazu, Abba Isah Muhammad na da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!