Connect with us

Labarai

Dakarun tsaftar muhalli: An baiwa hammata iska da mai sayar da abinci

Published

on

Hatsaniyar ta kaure ne tsakanin dakarun tsaftar muhalli na jihar Kano da wata mata mai sayar da abinci a unguwar Kabuga.

Ma’aikatan kula da tsaftar muhalli sun dai shiga gidan sayar da abinci ne domin duba yadda tsaftar muhallin wajen, wanda a ka yi zargin ma’aikatan gidan abinci su ka farwa ma’aikatan da duka, har su ka yagawa guda daga cikin ma aikatan riga.

Wakilin mu Mu’azu Musa Ibrahim ya tuntubi jagorar tafiyar na dakarun tsaftar muhallin ya ce”Mun iske gidan sayar da abincin kaca-kaca babu tsafta, wanda ma’aikatan gidan sayar da abincin su ka fara zagin mu, mu kuma mun fada mu su ga yadda za su gyara, kawai sai ji mu ka yi sun fara dukan mu”.  Inji Kwamrade Sadiku Muhammad Wada.

Wakilin mu ya tuntubi bangaren ma su sayar da abincin, amma sun ki cewa komai a kai, sakamakon lamarin na wajen ‘yansanda, ya kuma tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce za su bincika.

Labarai

Rahoto: Mu tuba ga Allah domin fita daga tsanani – Limamin Na’ibawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Nana Aisha da ke unguwar Na’ibawa Gabas, Malam Abubakar Jibril ya ce, al’umma su tuba zuwa ga Allah, domin ya musanya tsanani zuwa yanayi na walwala.

Malam Abubakar Jibril, ya bayyana hakan ne ta cikin Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke ƙasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rashin wadatar zuci ke janyo zalinta a tsakanin al’umma – Limamin CBN Quarters

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Faruq Unguwa Uku CBN Quarters, Dr. Aminu Ismai’l, ya ce, rashin wadatar zuci ke janyo zalunci da cutar wa a tsakanin al’umma.

Dr. Aminu Isma’il, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ke yi wa Dala FM ƙarin bayani dangane da Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu guji yin ƙarya da yaɗa ta – Limamin Chiranchi

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Sheikh Aliyu Harazimi da ke unguwar Chiranchi, a ƙaramar Hukumar Kumbotso, Dr Rabi’u Tijjani Rabi’u, ya ja hankalin al’ummar Musulmi da su guji yin ƙarya da kuma yaɗa ta.

Dr. Rabi’u ya bayyana hakan ne, yayin da yake ƙarin haske dangane da abin da huɗubar sa ta ƙunsa.

Wakilin mu na ƴan Zazu, Abba Isah Muhammad na da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!