Connect with us

Labarai

Iyaye ku kula da ‘ya’yan ku – Khalid Ishaq Diso

Published

on

Shugaban ƙaramar hukumar Gwale, Alhaji Khalid Ishaq Ɗiso ya ce, bai kamata iyaye su rinƙa nuna halin ko in kula da tarbiyyar ƴaƴansu ba, domin nuna hakan kan jefasu cikin wani hali.

Khalid Ishaq ya bayyana hakan ne a yayin Saukar karatun Alkur’ani mai girma na ɗalibai 54, da makarantar, Abdullahi Bin Mas’ud ta gudanar cikin unguwar Sharaɗa Rinji da ke yankin ƙaramar hukumar Gwale a ranar Asabar 09-10-2021.

Ya ce”Kamata ya yi iyaye su ƙara kulawa da tarbiyyar ƴaƴan na su, domin rayuwarsu ta zama abar koyi a cikin al’umma”. Inji Khalid.

Da yake nasa jawabin shugaban makarantar, Mallam Aliyu Abdallah Indabawa, ya ce”Makarantar ta na buƙatar tallafin ma su hannu da shuni bisa ƙalubalen da su ke fuskanta na rashin kyawun muhalli da kuma kayayyakin karatu, mu na neman agajin gwamnati da masu hannu da shuni”.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u, ya rawaito mana cewar, al’umma da dama ne su ka samu damar halartar bikin saukar, daga ciki kuwa akwai mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Alhaji Zubairu Hamza Massu, da kuma shugaban hukumar Karota Baffa Babba Ɗan Agundi.

Labarai

Rahoto: Dalibi ya kawo credit 9 a qualifying ya yi tsauri da yawa – Mai duba jarabawa

Published

on

Wani tsohon mai duba sakamakon jarabawar qualifying a jihar Kano ya ce, ana duba gazawar biyawa dalibai kudin jarabawar qualifying ne yayin fitar da sakamako, saboda haka akwai rashin adalci akan lallai sai dalibai sun kawo credit 9

Tsohon mai duba sakamakon jarabawar, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.

Muna da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Yadda hadarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2 a Lambu

Published

on

Wasu motoci babba da karama, sun yi taho mu gama akan titin garin Lambu da ke karamar hukumar Tofa a jihar Kano, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane biyu, daya kuma ya jikkata.

Wasu da al’amarin ya faru a gaban idanunsu, sun bayyanawa wakilin mu na ‘yan Zazu , Abubakar Sabo cewar, mai karamar motar ne ya yi a ran hannu, wanda ya janyo faruwar hadarin.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Babban Labari: Mun kama mota makare da kayan fashewa da bindugu da harsashi a Kano – Kiyawa

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sami nasarar cafke wata mota makare da wasu kayayyakin da ake hada abubuwan fashewa da kuma bindigu kirar AK47 .

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya ce, sun samu nasarar kama motar kirar Mercedez a unguwar Bubbugaje dake karamar hukumar Kumbotso.

A cewar Kiyawa sun sami rahoran sirri ne akan motar wadda suke zargin an kawo ta daga Jihar Jigawa zuwa Kano makare da irin kayayyakin da suke zargin da sune ake hada abubuwan fashewa domin aikata ta’addanci.

Sanarwar ta kuma ce bayan samun rahotan sirri na kara sowar motar zuwa Kano, jami’an tsaron Puff Adder suka yi wa mator kawanya, wanda hakan yasa mutanan ciki suka tsere suka bar motar a nan.

“Mun samu nasarar gano bindiga kirar AK47 guda biyu da kuma kananan bindigu biyu kirar Pistol tare da alburusai dubu daya da dari takwas”. In ji Kiyawa.

Continue Reading

Trending