Connect with us

Wasanni

Gago Challenge Cup: Wasan zagayen siri daya kwale

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Dabo Babies za ta fafata da Darma United a yammacin ranar Juma’a 22 ga watan Oktoba na wannan shekarar.

ga jerin sauran wasannin da za a fafata.

New Star Rijiyar Zaki da Chiranchi United ranar Asabar 23-10-2021

Soccer Strikers da Gwale United ranar Lahaddi 24-10-2021

Samba Kurna da Red Elephant ranar Juma’a 29-10-2021

Kano Municipal da Kano Ambassadors ranar Asabar 30-10-2021

Higihlanders da Top Star Panshekara ranar Lahadi 31-10-2021

Ashafa Action da Mujan Warrios ranar Juma’a 05-11-2021

Golden Bullet da Itihad Mandawari ranar Asabar 06-11-2021.

Manyan Labarai

Dalilan da ya sanya muka ɗauke Sadio Mane daga Liverpool – Oliver Khan

Published

on

Shugaban Bayern Munich, Oliver Kahn, ya bayyana dalilin da yasa kungiyar ta sayi Sadio Mane daga Liverpool.

Bayern Munich ta tabbatar da daukar Mane daga Liverpool a hukumance ranar Laraba.

Mane ya koma zakarun Bundesliga kan kwantiragin shekaru uku daga kungiyar Liverpool ta Premier.

A cikin wani sakon twitter da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, Kahn ya ce, manyan nasarorin da Mane ya samu a matakin kasa da kasa ya sa Bayern ta saye shi.

Ya wallafa a shafinsa na Twitter: “Muna farin ciki da cewa za mu iya lashe wasanni da Sadio #Mané na @FCBayern.

“Godiya ga fitattun ayyukansa da manyan nasarorin da ya samu a matakin kasa da kasa, ya kasance dan wasa tsawon shekaru da yawa da ba kasafai ake samunsa ba a duniya.”

Kwanan nan Mane ya lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka, AFCON, tare da tawagar kasar Senegal, kuma ya ba su damar shiga gasar cin kofin duniya na FIFA na bana a Qatar, yayin da ya samu nasarori da dama a Liverpool.

Continue Reading

Manyan Labarai

Liverpool ta amince Mane ya koma Bayern Munich

Published

on

Liverpool ta amince da cinikin Yuro miliyan 41 kwatankwacin Fam miliyan 35.1, domin siyar da Sadio Mane ga zakarun gasar Bundesliga Bayern Munich.

Liverpool za su sami ƙayyadaddun Yuro miliyan 32 kwatankwacin Fam miliyan 27.4, tare da ƙarin Yuro miliyan 6 dangane da bayyanar da Yuro miliyan 3.

Liverpool ta yi watsi da tayin biyu daga Bayern kafin ta amince da sabon tayin dan wasan mai shekaru 30, wanda yarjejeniyarsa za ta kare har zuwa bazara mai zuwa.

Mane ya koma Liverpool kan fan miliyan 31 da kuma fam miliyan 2.5 daga Southampton a shekarar 2016.

Labarin tafiyar tasa ya biyo bayan sayan dan wasan gaban Uruguay, Darwin Nunez daga Benfica a ranar Talata kan fam miliyan 64.

Continue Reading

Manyan Labarai

Tsohon dan wasan Liverpool da Holland ya zama sabon mai horaswa

Published

on

Tsohon dan wasan Liverpool da Netherlands, Dirk Kuyt ya fara aikinsa na babban koci tare da kungiar ADO Den Haag wadda ta ke buga gasar Eerste Divisie.

Kuyt, wanda ya buga wasan karshe na gasar zakarun Turai tare da Liverpool da kuma wasan karshe na cin kofin duniya tare da Holland, ya yi ritaya a matsayin kwararren dan kwallon kafa tare da Feyenoord a shekarar 2017.

Dan shekaru 41 ya yi aiki a kungiyar Quick Boys, a matsayin mataimaki da kuma Feyenoord, a tsarin matasan su, amma yana daukar matakinsa na farko a babban matsayi.

ADO ta tabbatar da kwantiragin shekara guda na Kuyt a ranar Alhamis, kuma ya ce: “ADO Den Haag babban kungiya ce, kuma ina matukar farin cikin kasancewa a nan a yau kuma na fara wannan sabon kalubale a matsayin koci.

“Ina godiya da irin tarba da kuma amanar da kulob din ya nuna min.

Continue Reading

Trending