Wasanni
Abusi Cup: Sakamakon gasar

Manyan Labarai
Da Duminsa: Klopp ya taya Guardiola murnar lashe Firimiya

Mai horas da Liverpool, Jurgen Klopp, ya taya kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, bisa lashe gasar kofin Firimiyar kasar Ingila da ta yi a kakar bana.
Manchester City ta lashe kofin Firimiya ne da maki daya kacal a kan Liverpool, wanda aka karkare gasar Man City na da maki 93 Liverpool na da maki 92.
“Ina taya ku murna ga Man City da Pep Guardiola, na gode wa Aston Villa da Wolverhampton, saboda yadda suka yi wasa mai kyau.”
“Ba sakamakon da muke so ba ne, dan wasan ne. Ban san ainihin sakamakon ba amma na san sun tashi 1-0 – shin sun tashi 2-0 kuma? Tabbas a halin yanzu akwai rashin jin daɗi. nan ma.
“Idan aka tashi 5-0 a City bayan mintuna 10 wasa ne kawai a gare mu. Ba wasanmu mafi kyau ba ne, amma duk yana da kyau.
Manyan Labarai
Jose Peseiro ya zama sabon mai horas da Super Eagles

Hukumar kwallon kafa ta ƙasa NFF, ta naɗa Jose Peseiro a matsayin sabon mai horas da tawagar Super Eagles.
Hukumar ta ce, Jose Peseiro wanda ɗan asalin ƙasar Portugal ne, shi zai jagoranci Super Eagles.
Mai magana da yawun ƙungiyar, Ademola Olajire, ya sanar da hakan ga manema a ranar Lahadi, ya ce, zai fara jagorantar tawagar Super Eagles a ziyarar da za ta kai Amurka a wasannin sada zumunci.
Manyan Labarai
Da Duminsa: Liverpool ta lashe kofin FA a hannun Chelsea

Liverpool ta samu damar lashe kofi na biyu a jere a hannun Chelsea, bayan da dan wasa Konstantinos Tsimikas ya raba fadan a bugun daga kai sai mai tsaron raga a gasar cin kofin FA Cup.
Liverpool ta lashe kofin Carabao Cup a hannun Chelsea a watannin baya a filin wasa na Wembley, sai ga shi a karo na biyu ta kuma lashe kofi a hannun ta, a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Mason Mount ya zubar da kwallo bayan da mai tsaron gidan Liverpool Alisson ya kade kwallon sa ta karshe a wasan, wanda ya baiwa Tsimikas damar baiwa Liverpool lashe kofin karo na 8.
-
Nishadi2 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai2 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai2 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai2 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Manyan Labarai2 years ago
Ba’amurkiya da masoyin ta sun hada cinkoso a kasuwar Sabon Gari