Connect with us

Wasanni

Kano Lions: Mu na mika sakon ta’aziya ga kungiyar Gwammaja United – Coach Amo

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Lions, ta mika sakon ta’aziyar ta ga mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Gwammaja United, Caoch Sagiru Sagi, bisa rasuwar Kakar sa.

Sanarwar mai dauke da jami’in hulda da jama’a na kungiyar, Injinya Abba Zubair, ta ce a madadin jagorancin shugaban kungiyar Sa’ad Ahmad Ma’aji Coach Amo, ta kuma yi addu’ar fatan shiga Aljanna tare da baiwa iyalanta baki daya hakurin juriya.

Wasanni

PSG: Har yanzu babu wata tattaunawa da Zidane – Leonardo

Published

on

Daraktan wasanni na kungiyar kwallon kafa ta PSG, Leonardo ya ce har yanzu mai horas da kungiyar, Mauricio Pochettino bai nemi barin kungiyar Paris Saint-Germain ba, kuma babu wata tattaunawa da su ka yi d da Zinedine Zidane.

Hasashe ya nuna cewa, Pochettino na daya daga cikin manyan masu horaswa da Manchester United ta ke nema, domin maye gurbin Ole Gunnar Solskjaer a matsayin koci.

Rahotanni sun bayyana cewa, Manchester United na neman Pochetino dan kasar Argentina a matsayin mai horaswar da zai maye gurbin Solksjaer.

Continue Reading

Wasanni

Liverpool za ta yi iya kokarin ta a kan Thiago Alcantara – Klopp

Published

on

Mai horas da Liverpool, Jurgen Klopp, ya yi alkawarin cewa Liverpool za ta yi duk mai yiwuwa, domin tabbatar da cewa dan wasan ta, Thiago Alcantara, ya kasance cikin koshin lafiya, domin ganin ya zama tauraro a duk lokacin da suke kokarin lashe gasar Premier.

Tsohon dan wasan Barcelona da Bayern Munich, Thiago ya koma Liverpool, sakamakon nasarar da su ka yi a gasar na kakar 2019-20.

Raunin da ya samu ya kawo cikas ga ci gabansa, kuma dan wasan mai shekara 30 dan kasar Spain ya yi kokarin nuna kyakykyawan yanayinsa akai akai.

Continue Reading

Wasanni

Horaswa: Manchester ta cimma yarjejeniya da Ralf Rangnick

Published

on

Manchester United na dab da nada Ralf Rangnick a matsayin kocin rikon kwarya a kan kwantiragin watanni Shida.

Mai horaswar ɗan kasar Jamus mai shekaru 63 a duniya, ya na shirin komawa Manchester United, amma ba zai jagoranci kungiyar a karshen wannan mako ba, a karawar da za ta yi da Chelsea yayin da ya ke jiran takardar izinin kama aiki.

Manchester United ta amince da yarjejeniya da Rangnick tsohon mai horas da RB Leipzig ta kasar Jamus, amma ba tare da kungiyar Lokomotiv Moscow ba, inda shi ne shugaban wasanni da ci gaba na kungiyar.

Hakan na zuwa ne bayan da Manchester United ta kori Ole Gunnar Solskjaer a ranar Lahadin da ta gabata, bayan shafe shekaru Uku a matsayin koci.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!