Labarai
Kano: Za a kara inganta aikin Baturen ‘yansanda da al’umma – DSP Kiyawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, za ta kara inganta tsarin aikin Baturen ‘yansanda tare da al’umma, saboda gudunmawar da Jama’a ke bayar wa wajen tabbatar da tsaro.
Mai Magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan, a zantawar sa da gidan rediyon Dala.
Ya na mai cewar, “Kwamishinan ‘yansandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya bai wa Baturen ‘yansandan umarnin aiki tare da al’ummar yankunan su, duba da muhimmancin su a fannin tsaro. Mutane na da damar kai korafi ofishin ‘yansanda, mafi kusa da su har zuwa Kwamishinan ‘yansanda jihar Kano ko na jami’in hulda da jama’a”. A cewar DSP Kiyawa.
Wakiliyar mu Aisha Shehu Kabara ta rawaito rundunar ‘yansandan jihar Kano, ta kuma gargadi mutane da su rinka lura da kai kawon baki fuska a yankunan su.

Labarai
Cutar mashako ta bulla a wasu sassan Jigawa

Akalla mutum goma ne suka mutu bayan ɓarkewar cutar mashaƙo a kananan hukumomi 14 na jihar Jigawa.
Ma’aikatar Lafiyar jihar ce ta sanar wa manema labarai haka a Dutse, a yau Lahadi. Ta ce ana kuma zargin cewa mutum 91 sun kamu da cutar.
Babban sakatare a ma’aikatar, Dr Salisu, Mu’azu, ya ce zuwa yanzu, an tabbatar da mutum biyu da suka kamu da cutar a kananan hukumomin Kazaure da Jahun yayin da aka Ɗauki jinin wasu zuwa Abuja domin yin gwaji da tantancewa.
Mu’azu ya ce ɓarkewar cutar abin damuwa ne musamman ma ganin cewa ta ɓulla a yankunan da ba su taɓa yin riga-kafin ta ba.
A cewarsa, tuni ma’aikatar ta fara bincike domin tattaro bayanai daga yankunan da abin ya shafa.
Ya ce gwamnatin jihar tuni ta fara shiri don yin riga-kafi a yankunan domin kaucewa yaɗuwar cutar.
Hangen Dala
Hukuncin kotu:- Zamu daukaka Kara – Abba Gida Gida

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yace zasu ɗauki matakin ɗaukaka ƙara zuwa gaba domin tabbatar da adalci kan hukuncin da kotun sauraron korafe-korafen zabe ta yanke inda ta ayyana Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan da aka gabatar a watan Maris din 2023.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya gudana a fadar gwamnatin Kano a daren laraba.
Gwamnan ya ƙara da cewa sun umarci lauyoyin su da su hanzarta wajen ɗaukaka ƙara ba tare da ɓata lokaci ba.
Ka zalika ya kuma ce wannan hukuncin bazai sanyar musu da gwiwa ba wajen ci gaba da gudanar da ayyukan da suka fara.
A ranar Laraba ne dai 20 ga watan Satumba 2023 kotun sauraron korafe-korafen zabe ta tabbatar da Nasiru Gawuna a matsayin Wanda ya lashe zaben Gwamnan Kano da aka gabatar a watan Maris. (more…)
Hangen Dala
Hukuncin zaben Kano:- An Kori ‘yan Jarida daga harabar kotu

Jami’an Ƴan Sanda sun hana ƴan Jarida shiga harabar Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe ta Kano.
Duk da asubanci da ƴan jarida suka yi, jami’an ƴan sanda sun yi ƙememe sun hana su shiga.
Ƴan sandan sun koro wakilan kafafen yaɗa labarai da dama zuwa can nesa da Kotun.
A yau ne dai za’a Yanke hukunci Kan karar da jam’iyyar APC ta shigar gaban kotun tana kalubalantar nasarar Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf.
Ƙarin bayani na tafe.
-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano