Connect with us

Ilimi

Wasa kwakwalwa: Ɗaliba ta lashe Keke a gasar hada kalmomi na Dawanau

Published

on

Shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Ado Tambai Ƙwa, ya ja hankalin iyaye da su ƙara kulawa da karatun ƴaƴansu, domin rayuwarsu ta zama abar koyi a tsakanin al’umma.

Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana hakan ne ta bakin wakilin sa, Alhaji Sa’idu Abdu Tumfafi a yayin taron gasar Spelling B da Ƙungiyar Ɗalibai da cigaban gari ta Dawanau DASCOSA ta shiryawa Ɗaliban Firamaren Bagadawa dake yankin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa wanda ya gudana a ranar Alhamis 18-11-2021.

Ya na mai cewa”Matuƙar iyayen za su ƙara kulawa da karatun ƴaƴansu, to kuwa babu makawa za a samu cigaban da ya dace a fannin karatun na su”. Inji Tambai Kwa.
Da ya ke nasa jawabin shugaban Ƙungiyar, Abubakar Tasi’u Dawanau, cewa ya yi, ƙungiyarsu ta shiryawa ɗaliban gasar Spelling B ne, domin ƙarfafa musu gwiwa a fannin karatun su”. Inji Alhaji Sa’idu.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, bayan kammala gasar dai an baiwa dalibar da ta zo na farko kyautar Keken ɗinki, sai kuma wacce ta zo ta biyu a ka ba ta kyautar keken hawa, yayin da kuma a ka baiwa dalibin da ya zo na Uku kyautar kuɗaɗe, waɗanda su ka rinƙa bayyana farin cikinsu.

Ilimi

Gwamnatin Kano ta kulla yarjejeniya da kasar Saudiyya a fannin ilimi

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta amince da wata yarjejeniya tsakanin Kano da Madina Academy da ke kasar Saudiyya, domin horar da malamai 5,000 a Madina.

Kwamishinan yada labarai, Muhammad Garba ne ya sanar da hakan a yayin ganawa da manema labarai kan sakamakon taron majalisar zartarwar jihar na jihar.

Gwamnatin za ta dauki nauyin bayar da tikitin dawowar jirgi da biza da alawus na horo ga rukunin farko na malamai 50 da za su halarci babban horo a Madina kafin watan Ramadan.

Gwamnatin ta kuma amince da fitar da Naira miliyan 94.9 domin saukaka matsugunin shagunan haya da gareji a kasar Saudiyya na shekarar 2020 da 2021.

Continue Reading

Ilimi

Ya kamata mu san tarihin yankunan mu – Dagacin Zawaciki

Published

on

Dagacin garin Zawaci dake yankin karamar hukumar Kumbosto, Mallam Abdulkadir Mu’azu, ya ce, kamata al’umma su kara himma wajen sanin tarihin garinsu, domin mahimmancin da hakan ya ke dashi.

Mallam Abdulkadir ya bayyana hakan ne a yayin taron kaddamar da littafin tarihin garin Zawaciki, wanda wani matashi mai suna Abubakar Yahuza Yakubu ya rubuta, wanda a ka gudanar cikin dakin taro na Islamic Center a ranar Asabar din nan.

Da ya ke nasa jawabin marubucin littafin Abubakar Yahuza Yakubu, bayyana dalilan da ya ce, ya rubuta littafin tarihin ne, domin mahimmancin da hakan yake dashi.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u da ya samu damar halartar taron ya rawaito mana cewar, alumma da dama ne suka samu damar halartar taron, kuma ciki har da tsohon shugaban karamar hukumar Kumbosto Kabiru Ado Panshekara.

Continue Reading

Ilimi

Karancin tallafawa makarantun Islamiyya ya kan haifar da matsala – Wakilin Arewa

Published

on

Wakilin Arewa dake cikin birnin Kano, Sayyadi Muhammad Yola ya ce, karancin rashin taimakon da masu hannu da shuni ke yi ga makarantun Islamiyya, yakan kawo tabarbarewar tarbiyar matasa a halin yanzu.

Sayyadi Muhammad ya yi wannan jawabin ne a yayin saukar karatun Al-kur’ani mai girma na makarantar, Subulussalam Kur’an Islamiyya ta gudanar cikin unguwar kofar ruwa na dalibai 204.

Da ya ke nasa jawabin shugaban makarantar Malam Anas Mahamud Madabo, ya ce, sau tari sukan fuskanci kalubale ta wajen iyayen dalibai, musamma ma wajen karancin biyan kudin makarantar, domin haka ya ke kira a garesu da su kara himma wajen biyan.

Wakiliyar mu, Aisha Ibrahim Abdul, ta rawaito cewar a cikin daliban da su ka yi saukar akwai matan aure guda Arba’in da Biyu.

Continue Reading

Trending