Connect with us

Labarai

Rahoto: Mu yi haƙuri da tsadar rayuwar da mu ke ciki – Limamin Kabuga

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Abdullahi Bin Mas’ud, da ke unguwar Kabuga ‘Yan Azara, Malam Zakariyya Abubakar, ya ce, al’umma sai sun yi haƙuri da jarabawar tsadar rayuwa da a ke ciki, domin duk mai haƙuri zai samu lada ba tare da ƙididdiga ba.

Yayin da ya ke yi wa wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Ɗinki ƙarin bayani, Malam Zakariyya ya kuma ce, sai mutane sun kasance masu imani da aiki nagari da gaskiya, sannan za a samu dacewa.

Wakilin namu na ɗauke da cikakken rahoton huɗubar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Rahoto: Mu tuba ga Allah domin fita daga tsanani – Limamin Na’ibawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Nana Aisha da ke unguwar Na’ibawa Gabas, Malam Abubakar Jibril ya ce, al’umma su tuba zuwa ga Allah, domin ya musanya tsanani zuwa yanayi na walwala.

Malam Abubakar Jibril, ya bayyana hakan ne ta cikin Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke ƙasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rashin wadatar zuci ke janyo zalinta a tsakanin al’umma – Limamin CBN Quarters

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Faruq Unguwa Uku CBN Quarters, Dr. Aminu Ismai’l, ya ce, rashin wadatar zuci ke janyo zalunci da cutar wa a tsakanin al’umma.

Dr. Aminu Isma’il, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ke yi wa Dala FM ƙarin bayani dangane da Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu guji yin ƙarya da yaɗa ta – Limamin Chiranchi

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Sheikh Aliyu Harazimi da ke unguwar Chiranchi, a ƙaramar Hukumar Kumbotso, Dr Rabi’u Tijjani Rabi’u, ya ja hankalin al’ummar Musulmi da su guji yin ƙarya da kuma yaɗa ta.

Dr. Rabi’u ya bayyana hakan ne, yayin da yake ƙarin haske dangane da abin da huɗubar sa ta ƙunsa.

Wakilin mu na ƴan Zazu, Abba Isah Muhammad na da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!