Connect with us

Labarai

Rikicin APC: Tunda Shekarau ya ke bai taɓa taimakon Jam’iyya ba – Abdullahi Abbas

Published

on

Shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano, Hon. Abdullahi Abbas ya ce, Sanatan Kano ta tsakiya, malam Ibrahim Shekarau bai taɓa taimakon jam’iyyar ba, tun bayan ɗarewar sa kan kujerar Sanata.

Hon. Abdullahi Abbas ya bayyana hakan ne, yayin wani taron manema labarai, a ranar Laraba.

Ya ce, “Jam’iyyar APC ita ce ta taimaka wa Sanata Shekarau, amma sai sau ɗaya lokacin Sallah, Shekarau ya bai wa jam’iyya Dubu Ɗari”.

Ya kuma ce, “Mu muka tura shi, ƙarshe ya ci moriyar Ganga, ba wanda ya ke amfanar sa sai shi kaɗai da iyalan sa, amma Jam’iyya ba ta amfanar Malam Shekarau “. A cewar Abdullahi Abbas.

Ho. Abdullahi Abbas, ya kuma ƙara da cewa, jam’iyya ce ta yi masa riga da wando, amma shi ba ya taimaka ma ta da komai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Rahoto: Mu tuba ga Allah domin fita daga tsanani – Limamin Na’ibawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Nana Aisha da ke unguwar Na’ibawa Gabas, Malam Abubakar Jibril ya ce, al’umma su tuba zuwa ga Allah, domin ya musanya tsanani zuwa yanayi na walwala.

Malam Abubakar Jibril, ya bayyana hakan ne ta cikin Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke ƙasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rashin wadatar zuci ke janyo zalinta a tsakanin al’umma – Limamin CBN Quarters

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Faruq Unguwa Uku CBN Quarters, Dr. Aminu Ismai’l, ya ce, rashin wadatar zuci ke janyo zalunci da cutar wa a tsakanin al’umma.

Dr. Aminu Isma’il, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ke yi wa Dala FM ƙarin bayani dangane da Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu guji yin ƙarya da yaɗa ta – Limamin Chiranchi

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Sheikh Aliyu Harazimi da ke unguwar Chiranchi, a ƙaramar Hukumar Kumbotso, Dr Rabi’u Tijjani Rabi’u, ya ja hankalin al’ummar Musulmi da su guji yin ƙarya da kuma yaɗa ta.

Dr. Rabi’u ya bayyana hakan ne, yayin da yake ƙarin haske dangane da abin da huɗubar sa ta ƙunsa.

Wakilin mu na ƴan Zazu, Abba Isah Muhammad na da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!