Connect with us

Wasanni

Da yiwuwar dawowar Arsene Wenger zuwa Arsenal – Arteta

Published

on

Mai horas da Arsenal, Mikel Arteta ya ce ya na son dawo da tsohon mai horas da Arsenal, Arsene Wenger, a wani matsayi, kuma tuni ya yi magana da shi kan yiwuwar dawowar sa.

Wenger, mai shekaru 72, ya jagoranci Arsenal ta lashe gasar Premier har sau Uku, sannan ya lashe kofin FA sau Bakwai a cikin shekaru 22 da ya yi ya na jan ragamar kungiyar da ke Arewacin London.
Arteta wanda ya shafe tsawon shekaru Biyar ya na taka leda a karkashin Wenger a kungiyar ta Aresenal.

Arteta ya ce “Za mu yi farin cikin samun kusanci da shi. Ina ganin zai yi matukar farin ciki ganin yanayin da zai iya haifarwa a kusa da shi, idan ya na kusa da wannan wurin, saboda mutuntawa, sha’awa da kuma soyayyar da kowa a kungiyar din ya ke yi na abin da ya yi, da kuma abin da ya yi. . Abin da zan iya cewa daga gefena ne kuma zan iya cewa, a madadin kowa da kowa, za mu yi farin cikin samun shi sosai”.

Mikel Arteta ya maye gurbin Unai Emery a matsayin kocin Gunners a watan Disamba na 2019, watanni 19, bayan Wenger ya yi wasanni 1,235 a matsayin kocin Arsenal ya kawo karshen kakar wasa ta 2017-18.

Arteta ya jagoranci kungiyar zuwa nasarar cin Kofin FA a 2019-20, amma bayan kammala matsayi na Biyu a jere a matsayi na Takwas a gasar Premier a bara, Gunners ta kasa samun cancantar shiga gasar Turai a karon farko tun cikin shekaru 25.

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending