Connect with us

Wasanni

Ballon d’Or: Cristiano ya caccaki masu bayar da kyautar

Published

on

Cristiano Ronaldo ya zargi editan kwallon kafa na Faransa da yin karya bayan ya ce burin dan kasar Portugal shi ne ya yi ritaya da karin kyautar Ballon d’Or fiye da Lionel Messi.

Mai shirya Ballon d’Or Pascal Ferre ne ya yi wannan ikirarin ga jaridar New York Times.

A ranar Litinin ne Messi na Paris St-Germain ya lashe kyautar Ballon d’Or karo na bakwai, yayin da Ronaldo wanda ya lashe sau biyar ya zo na shida.
Ronaldo ya ce “A ko da yaushe ina yin nasara ga kaina da kuma kungiyoyin da na ke wakilta. Na yi nasara ga kaina da kuma wadanda suke so na, ba na cin nasara a kan wani.”

A ranar Juma’a, Ferre ya shaida wa jaridar New York Times cewa: “Ronaldo ya na da buri daya kacal, kuma shi ne ya yi ritaya da karin Ballon d’Or fiye da Messi, kuma na san hakan saboda ya fada min”.

Ronaldo ya mayar da martani a shafukan sada zumunta inda ya ce: “Pascal Ferre ya yi karya, ya yi amfani da sunana wajen tallata kansa da kuma tallata littafin da ya ke yi wa aiki. Ba abin yarda ba ne cewa mutumin da ke da alhakin bayar da irin wannan babbar kyautar zai iya yin karya ta wannan hanyar, ba tare da mutunta wanda ya taba mutunta kwallon kafa ta Faransa Football da Ballon d’Or ba. Babban burina a rayuwata shi ne na lashe kofunan kasa da kasa a kungiyoyin da na ke wakilta da kuma ‘yan wasan kasa a kasata. Babban burina a rayuwata shine in bar sunana a rubuce a cikin haruffan zinare a tarihin kwallon kafa na duniya.”

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending