Connect with us

Labarai

Kotu: Mu na nazari a kan wannan hukuncin – Ganduje

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Ganduje, ya yi kira ga magoya bayansa a jam’iyyar APC mai mulki a jihar da su kwantar da hankalinsu tare da bin hanyar zaman lafiya da bin doka da oda.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a matsayin martani ga hukuncin da wata babbar kotun Abuja ta yanke ranar Juma’a, wanda ya nuna goyon bayan tsagin Malam Ibrahim Shekarau na G7 na jam’iyyar APC.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba ya fitar, a ranar Juma’a, gwamnan ya ce” Tunda lamarin na cikin jam’iyya ne, gwamnati da jam’iyyar APC a halin yanzu muna nazari kan lamarin, domin samun mafita”.

Gwamna Ganduje ya kuma umurci jami’an tsaro da kada su lamunci rashin bin doka da oda, domin gwamnati ba za ta amince da duk wani aika-aika da ta’addanci ko tashin hankali a wani yanki na jihar ba, da sunan siyasa ko wani fage.

Sanarwar ta kuma nuna godiya ga ‘yan jam’iyyar a dukkan matakai da sauran masu ruwa da tsaki bisa jajircewar da su ka nuna wajen marawa jam’iyyar baya.

Labarai

Rahoto: Dokar hana shan shisha ta fara aiki gadan-gadan a Kano – Hisba

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simamen shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama dillalan Shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita.

A zantawar daya daga cikin masu shagunan sayar da Shisha da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, ya bayyana cewar, ya yi tunanin dokar hana shan Shisha ta tsaya kan masu wuraren shan Shisha ba masu sayarwa ba.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Shekaru 10 ina sarrafa Turoso amma ko ciwon kai ban taba yi ba – Mai Turoso

Published

on

Wani magidanci mai sana’ar sarrafa Turoso a yankin Kududdufawa ya ce, sama da shekaru goma ya na aikin sarrafa Turoso, amma ko ciwon kai bai taba yi ba.

Malam Isah Musa Katsinawa mazunin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Gobara ta lakume ran mutane 3 ciki harda dattijuwa

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ta kai tallafi wani gida da aka samu iftila’in gobara, wanda ta yi sanadiyar rasa mutane Uku  a unguwar Gama A, da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin mu na ‘yan zazu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, hukumar karkashin shugabanta Salihu Aliyu Jili, ta kuma kai tallafi gidan iyayen Hanifa, dalibar da aka yi zargin malaminta ya kashe ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending