Connect with us

Wasanni

Champions League: Kwallon Messi ta zama mafi kyau a matakin rukuni

Published

on

A Yunkurin da Lionel Messi ya yi wa Paris Saint-Germain da Manchester City an zabe shi a matsayin kwallon sa da ta fi kowacce kyau a gasar zakarun Turai a matakin rukuni.

Kwallon Messi mai shekaru 34 da ya ci wa PSG bayan da ya koma kyauta saboda matsalar kudi da Barcelona ta zama ta daya a gasar.

PSG ta tashi 1-0 a minti na takwas da fara tamaula daga dan wasan tsakiya Idrissa Gueye lokacin da Messi, a minti na 74 ya buga da kyar daya da biyu da Kylian Mbappe a gefen akwatin.

Bafaranshen ya koma kan hanyar Messi kafin dan wasan na Argentina ya bua wani bugun daga kai sai mai tsaron gida a kusurwar dama ta sama da Ederson wanda bai iya tare ta ba a ragar City.

Messi ya samu kashi 22 cikin 100 na kuri’un da aka kada – sama da 200,00 ne aka kada – bayan da Thiago Alcantara da Robert Lewandowski, wadanda suka samu kashi 14 da kashi 13 cikin 100, bi da bi.

Thiago ya farke kwallon da Liverpool ta ci Porto da ci 2-0 a filin wasa na Anfield, yayin da Lewandowski ya zura kwallo a wasan da Bayern Munich ta doke Dynamo Kiev da ci 2-1.

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending