Connect with us

Labarai

Ganduje ya rattaba hannu a kan kasafin shekarar 2022

Published

on

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya rattaba hannu a kasafin kudin shekarar 2022 a kan kudi fiye da Naira biliyan 221, bayan da majalisar dokokin Kano ta kammala aiki a kansa.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce, abin a yabawa majalisar dokokin Kano ne bisa ga gayyatar rukunin al’umma, domin fadar albarkacin bakin su a kan kasafin.

Ganduje ya ce”Kasafin an yi shi ne, domin kammala manyan ayyuka ba tare da barin bashi ga gwamnatin mai zuwa ba, shekara mai zuwa za a kama aiki, domin tabbatar da kammala dukkan ayyuka inda dokar kasafin kudin za ta fara aiki ne a daya ga watan Janairun shekara mai kamawa”.

A nasa awabin shugaban majalisar dokokin Kano, HamIsu Ibrahim chidari ya ce,”An samu Kari a kasafin, bisa ga bijirowar wasu ayyukan”.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta rawaito cewa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kuma godewa majalisar dokokin bisa ga kyakkyawar alakarta da gwamnatin Kano.

Labarai

Rahoto: Dokar hana shan shisha ta fara aiki gadan-gadan a Kano – Hisba

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simamen shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama dillalan Shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita.

A zantawar daya daga cikin masu shagunan sayar da Shisha da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, ya bayyana cewar, ya yi tunanin dokar hana shan Shisha ta tsaya kan masu wuraren shan Shisha ba masu sayarwa ba.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Shekaru 10 ina sarrafa Turoso amma ko ciwon kai ban taba yi ba – Mai Turoso

Published

on

Wani magidanci mai sana’ar sarrafa Turoso a yankin Kududdufawa ya ce, sama da shekaru goma ya na aikin sarrafa Turoso, amma ko ciwon kai bai taba yi ba.

Malam Isah Musa Katsinawa mazunin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Gobara ta lakume ran mutane 3 ciki harda dattijuwa

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ta kai tallafi wani gida da aka samu iftila’in gobara, wanda ta yi sanadiyar rasa mutane Uku  a unguwar Gama A, da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin mu na ‘yan zazu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, hukumar karkashin shugabanta Salihu Aliyu Jili, ta kuma kai tallafi gidan iyayen Hanifa, dalibar da aka yi zargin malaminta ya kashe ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending