Connect with us

Manyan Labarai

Manchester City ta hau teburi da maki 6

Published

on

Manchester City ta tsallake rijiya da baya bayan da ta doke Leicester City da ci 6-3 a karawar da su ka yi a ranar Boxing Day a filin wasa na Etihad.

Man City nai da maki shida a saman teburin gasar Premier bayan nasarar da su ka yi a jere a karo na tara, inda Liverpool da ke matsayi na biyu ba ta buga wasa ba.

Kevin De Bruyne ne ya fara zura kwallon farko a ragar kungiyar a cikin mintuna 25 da fara wasa, yayin da Riyad Mahrez da Raheem Sterling su ka zura a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Foxes sun dawo da karsashi bayan an dawo daga hutun rabin lokaci yayin da James Maddison, Ademola Lookman da Kelechi Iheanacho su ka yi barazanar dawowar da ba za a iya yi ba, amma Aymeric Laporte da Sterling sun dawo da Citizens kan turba kuma su ka samu maki.

Labarai

Rahoto: Dokar hana shan shisha ta fara aiki gadan-gadan a Kano – Hisba

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simamen shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama dillalan Shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita.

A zantawar daya daga cikin masu shagunan sayar da Shisha da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, ya bayyana cewar, ya yi tunanin dokar hana shan Shisha ta tsaya kan masu wuraren shan Shisha ba masu sayarwa ba.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Shekaru 10 ina sarrafa Turoso amma ko ciwon kai ban taba yi ba – Mai Turoso

Published

on

Wani magidanci mai sana’ar sarrafa Turoso a yankin Kududdufawa ya ce, sama da shekaru goma ya na aikin sarrafa Turoso, amma ko ciwon kai bai taba yi ba.

Malam Isah Musa Katsinawa mazunin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Gobara ta lakume ran mutane 3 ciki harda dattijuwa

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ta kai tallafi wani gida da aka samu iftila’in gobara, wanda ta yi sanadiyar rasa mutane Uku  a unguwar Gama A, da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin mu na ‘yan zazu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, hukumar karkashin shugabanta Salihu Aliyu Jili, ta kuma kai tallafi gidan iyayen Hanifa, dalibar da aka yi zargin malaminta ya kashe ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending