Connect with us

Labarai

Za a yi jana’izar Alhaji Bashir Othman Tofa a Kano

Published

on

Rahotanni daga makusantan, Alhaji Bashir Othman Tofa, sun tabbatar da cewa za a yi jana’izar marigayin a gidan sa da ƙarfe 9:00 na safiya da ke Gandun Albasa.

Tsohon dan takarar shugaban Najeriya Alhaji Bashir Othman Tofa ya rasu ne da asubahin nan a asibitin Malam Aminu Kano ya na da shekara 74 a duniya.

Wasu makusantansa sun tabbatar da cewa tsohon dan siyasar ya sha fama da jinya.

A makon jiya ne a ka yi ta yaɗa labarin cewa Bashir Tofa ya rasu, amma daga bisani a ka tabbatar bai rasu ba.

Alhaji Bashir Tofa, wanda fitaccen dan kasuwa ne kuma marubuci, ya bar mata da ‘ya’ya da dama.

An haife shi a birnin Kano ranar 20 ga watan Yunin 1947, kuma ya yi karatunsa a Najeriya da kuma Ingila.

Marigayin ya tsunduma harkokin siyasa a shekarar 1976, inda ya zama Kansila a karamar hukumar Dawakin Tofa a 1977.

Tun daga wancan lokacin ya rike mukamai da dama na siyasa ciki har da Sakataren jam’iyyar NPN reshen jihar Kano.

Bashir Othman Tofa ya tsaya takarar shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar NRC a zaben shugaban kasar da a ka gudanar a shekarar 1993.

Sai dai ya sha kaye a hannun Cif MKO Abiola na jam’iyyar SDP a zaben, wanda daga bisani gwamnatin soji karkashin jagorancin Janar Ibrahim Babangida, ta soke shi.

Marigayin, wanda shi ne shugaban kungiyar dattawan jihar Kano, ya na cikin dattijan Arewacin Najeriya da suka dade suna kokawa kan matsalar rashin tsaron da ke addabar yankin.

A wata hira da BBC Hausa, ya shaida mana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ya daukar shawarar da suke ba shi domin shawo kan matsalar.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending