Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Radadin Talauci: Amurka ta baiwa Afghanistan dala miliyan 308

Published

on

Gwamnatin Joe Biden na Amurka na shirin bayar da gudunmuwar karin dala miliyan 308 a matsayin taimakon jin kai ga Afghanistan, wanda zai kawo jimillar taimakon da Amurka ke bayarwa ga kasar da ke fama da talauci da kuma ‘yan gudun hijirar Afghanistan da ke yankin zuwa kusan dala miliyan 782 tun daga watan Oktoba.

Fadar White House ta kara da cewa, Amurka ta na kuma samar da karin alluran rigakafin cutar coronavirus miliyan daya zuwa Afghanistan, wanda ya kawo adadin miliyan 4.3.

Taimakon da hukumar raya kasa da kasa ta Amurka za ta bayar, ta hanyar kungiyoyin jin kai masu zaman kansu, domin samar da matsuguni da kula da lafiya da taimakon sanyi da agajin abinci na gaggawa da ruwa da kuma tsaftar muhalli, in ji gwamnatin.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutane miliyan 23 na kashi 55% na al’ummar kasar  Afghanisatn ke fuskantar matsananciyar yunwa, inda kusan mutane miliyan 9 ke fuskantar barazanar yunwa yayin da lokacin sanyi ke kankama.

Rikicin tattalin arzikin Afganistan ya kara tsananta, bayan da ‘yan Taliban su ka kwace mulki a watan Agusta, yayin da tsohuwar gwamnatin da kasashen Yamma ke marawa baya, sannan sojojin Amurka na karshe su ka janye.

A watan da ya gabata, Amurka a hukumance ta kebe jami’an Amurka da na Majalisar Dinkin Duniya da ke kasuwanci da ‘yan Taliban daga takunkumin Amurka, domin kokarin kiyaye kwararar kayan agaji zuwa Afganistan yayin da ta shiga cikin mawuyacin hali.

 

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji Sun yi juyin Mulki a Gabon

Published

on

Sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon tare da sanar da karbi mulki.

Sun ce sun soke sakamakon zaben da ka gudanar ranar Asabar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zaben ta ce Mr Bongo ya samu nasara ne da kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.

Sun Kuma ce Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalan gidansu ke yi a Gabon.

Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin dake sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa dukkan hukumomin kasar.

Daya daga cikin sojojin ya fada a tashar talabijin ta Gabon 24 cewa, “Mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ake yi a yanzu.”

Mr Bongo ya hau karagar mulki lokacin da mahaifinsa Omar ya rasu a shekara ta 2009.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji sunyi juyin Mulki a jamhuriyar Nijar

Published

on

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa Sojojin Kasar sun yi juyin Mulki, tare da sanar da kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum.

Cikin sanarwar da suka bayar a gidan telebijin din Kasar, jagoran tawagar sojojin Kanal Amadu Abdramane yace “mun kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum tare da karbe dukkanin Wani Iko”.

Sojojin dai sun bayar da dalilin halin rashin tabbas da Kuma Matsin tattalin arziki a kasar.

Tuni dai sojojin suka garkame dukkanin iyakokin Kasar tare da Sanya dokar takaita zirga zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Tun a safiyar laraba ne dai aka wayi gari da fara wancan yunkuri, Wanda yanzu haka ta tabbata, Kasar Nijar na hannun sojoji, Wanda shi ne Karo na hudu ana gudanar da juyin mulkin a jamhuriyar Nijar.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

An tsaurara tsaro a fadar shugaban Kasar Nijar

Published

on

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar, na nuni da cewa dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasa sun rufe duk wata hanyar shiga fadar a wani lamari da ba a kai ga ganowa ba.

Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasar ta Nijar na tattaunawa da sojojin domin sasanta lamarin.

Karin bayani nan tafe….

Continue Reading

Trending