Connect with us

Labarai

KAROTA da Adaidaita: Za mu dauki matakin shari’a idan ba a yi sulhu ba – Kungiyar Kare Hakki

Published

on

Shugaban kungiyar kare hakkin dan adam ta lobal Community for Human Right Network, Ambasada Karibu Yahya Lawan Kabara, ya ce, za su dauki matakin shari’a ga hukumar KAROTA, matukar bata samu dai-daito a tsakaninta da Direbobin baburan Adai-daita Sahu ba.

Ambasada Karibu Kabara ya yi wannan jawabin ne a yayin taron manema labarai da ya gudana a yau Talata a ofishin kungiyar da ke unguwar Sharada.

Ya na mai cewa, “Kamata ya yi shugaban hukumar lura da zirga-zirgar ababen hawa KAROTA, Baffa Babba Dan Agundi, ya samu damar zama da matuka baburan domin samun masalaha a tsakani.

Ya kuma ce, “Fara shigowar bakin fuska masu Babura mai kafa biyu da su ke aikin Achaba a gari, biyo bayan tsunduma yajin aikin da Direbobin baburan Adai-daita Sahun su ka yi, kan iya janyo matsalar tsaro”.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam, Ambasada Karibu Yahya Lawan Kabara, ya ce, matuka baburan yakamata su hakurkurtar da zuciyoyinsu dan ganin komai ya koma dai-dai.

Labarai

Rahoto: Dokar hana shan shisha ta fara aiki gadan-gadan a Kano – Hisba

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simamen shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama dillalan Shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita.

A zantawar daya daga cikin masu shagunan sayar da Shisha da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, ya bayyana cewar, ya yi tunanin dokar hana shan Shisha ta tsaya kan masu wuraren shan Shisha ba masu sayarwa ba.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Shekaru 10 ina sarrafa Turoso amma ko ciwon kai ban taba yi ba – Mai Turoso

Published

on

Wani magidanci mai sana’ar sarrafa Turoso a yankin Kududdufawa ya ce, sama da shekaru goma ya na aikin sarrafa Turoso, amma ko ciwon kai bai taba yi ba.

Malam Isah Musa Katsinawa mazunin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Gobara ta lakume ran mutane 3 ciki harda dattijuwa

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ta kai tallafi wani gida da aka samu iftila’in gobara, wanda ta yi sanadiyar rasa mutane Uku  a unguwar Gama A, da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin mu na ‘yan zazu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, hukumar karkashin shugabanta Salihu Aliyu Jili, ta kuma kai tallafi gidan iyayen Hanifa, dalibar da aka yi zargin malaminta ya kashe ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending