Connect with us

Labarai

KAROTA ta yi martani a kan dokar sabunta lasisi tukin ‘yan Adaidaita

Published

on

Hukumar KAROTA, ta ce duk wanda bai fahimci dokar hukumar sashi na goma da ya ba ta damar sabunta lasisin tuki ga masu ababen hawa na haya a jihar Kano, to ya na iya tafiya kotu domin neman nasara.

Lauyan hukumar KAROTA, Barista Mutawakkilu Muhammad Ishak a ganawarsa da manema labarai yau a ofoshin hukumar ne ya tabbatar da hakan.

Ya ce, “Dokar ta baiwa bangaren zartarwa ne damar tsara yadda za a aiwatar da ita, wanda kuma hukumar ta KAROTA ta na cikin bangaren na zartarwa da ta ke da alhaki a kan sufurin ababan hawa a jihar Kano gaba daya.

Ya kuma ce, “Ba wai iya masu Adaidaita Sahu kawai dokar ta shafa ba, har da duk sauran masu ababen hawa na haya a duk fadin jihar Kano”. A cewar Barista Mutawakil.

 

Labarai

Rahoto: Dokar hana shan shisha ta fara aiki gadan-gadan a Kano – Hisba

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simamen shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama dillalan Shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita.

A zantawar daya daga cikin masu shagunan sayar da Shisha da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, ya bayyana cewar, ya yi tunanin dokar hana shan Shisha ta tsaya kan masu wuraren shan Shisha ba masu sayarwa ba.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Shekaru 10 ina sarrafa Turoso amma ko ciwon kai ban taba yi ba – Mai Turoso

Published

on

Wani magidanci mai sana’ar sarrafa Turoso a yankin Kududdufawa ya ce, sama da shekaru goma ya na aikin sarrafa Turoso, amma ko ciwon kai bai taba yi ba.

Malam Isah Musa Katsinawa mazunin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Gobara ta lakume ran mutane 3 ciki harda dattijuwa

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ta kai tallafi wani gida da aka samu iftila’in gobara, wanda ta yi sanadiyar rasa mutane Uku  a unguwar Gama A, da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin mu na ‘yan zazu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, hukumar karkashin shugabanta Salihu Aliyu Jili, ta kuma kai tallafi gidan iyayen Hanifa, dalibar da aka yi zargin malaminta ya kashe ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending