Connect with us

Labarai

‘Yan sanda sun kama mutane 63 tun fara yajin Adaidaita Sahu

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce tun daga ranar Litinin ɗin da matuƙa baburan Adai-daita Sahu suka fara yajin aiki zuwa yau Laraba, ta kama aƙalla Mutane 63 da zargin cin zarafin masu ababen hawa.

Kakakin rundunar ƴan sandan, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan ga manema labarai da yammacin wannan rana ta Laraba.

DSP Kiyawa ya ce”Zuwa yanzu tuni mu ka miƙa mutanen gaban kotu, domin su girbi abinda su ka shuka”.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, rundunar ƴan sandan ta kuma yi kira da masu baburan Adai-daita Sahu, da su fito su cigaba da gudanar da ayyukan su na yau da kullum, inda kuma ta yabawa al’umma bisa haɗin kan da suke baiwa jami’ansu

Labarai

Rahoto: Mu nisanci abinda Allah Ya hana domin samun saukin rayuwa – Limamin Tukuntawa

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Masjidul Kuba da ke unguwar Tukuntawa a jihar Kano, Malam Ahmad Ali, ya ce, al’umma su duba tsakanin su da Allah tare da nisantar abinda ya hana, domin saukin tsadar rayuwa.

Malam Ahmad Ali, ya bayyana hakan ne, yayin da yake yiwa wakilin mu na ‘yan Zazu,  Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, Karin bayani dangane da abinda hudubar da ya gabatar ta kunsa.

Akwai cikakken bayanin hudubar a muryar da ke kasa.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rubutu na da muhimmanci a mu’amalar bashi – Limamin Bompai

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke unguwar Bompai, SP Abdulkadir Haruna, ya ce, akwai bukatar mu rinka gudanar da mu’amalar bashi yadda addinin musulunci.

SP Abdulkadir Haruna, yana bayyana hakan, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Abba Isah Muhammad, bayar idar da Sallar Juma’a.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashi ya yi yunkurin cinye tabar Wiwin da aka kama shi da ita a hanyar kotu

Published

on

Ana zargin wani matashi ya yi yunkurin hadiye tabar Wiwi da miyagun kwayoyi da aka kama shi da ita a hanyar kotu.

Tunda fari jami’an tsaron, sun kama matasahin da zargin samun sa da kayan maye, inda yake boye da wasu basu sani ba, kafin kuma a kai shi kotu, ya ciro su yana yunkurin hadiye wa.

Wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki yana da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending