Connect with us

Labarai

Rahoto: Kotu ta fara sauraron karar matashin da ake zargi da fasa gilashin Adaidaita

Published

on

Wani matashi ya gurfana a gaban kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a karamar hukumar Ungoggo, da laifin fasa wani gilas Adaidaita Sahu da kuma lalata shi, saboda zargin ya fito aiki a lokacin da ake yajin aikin ‘yan Adaidaita Sahun.

Direban da ake zargin an lalatawa Adaidaita Sahun, mai suna Auwal Aminu, ya bayyana wa wakilin mu na ‘yan Zazu Yusuf Nadabo Isma’il cewar, ya fito gyaran Adaidaita Sahun ne, mai gyaran bai fito ba, sai matashin ya dauki dutse ya fasa masa gilashi.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Labarai

Rahoto: Dokar hana shan shisha ta fara aiki gadan-gadan a Kano – Hisba

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simamen shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama dillalan Shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita.

A zantawar daya daga cikin masu shagunan sayar da Shisha da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, ya bayyana cewar, ya yi tunanin dokar hana shan Shisha ta tsaya kan masu wuraren shan Shisha ba masu sayarwa ba.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Shekaru 10 ina sarrafa Turoso amma ko ciwon kai ban taba yi ba – Mai Turoso

Published

on

Wani magidanci mai sana’ar sarrafa Turoso a yankin Kududdufawa ya ce, sama da shekaru goma ya na aikin sarrafa Turoso, amma ko ciwon kai bai taba yi ba.

Malam Isah Musa Katsinawa mazunin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Gobara ta lakume ran mutane 3 ciki harda dattijuwa

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ta kai tallafi wani gida da aka samu iftila’in gobara, wanda ta yi sanadiyar rasa mutane Uku  a unguwar Gama A, da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin mu na ‘yan zazu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, hukumar karkashin shugabanta Salihu Aliyu Jili, ta kuma kai tallafi gidan iyayen Hanifa, dalibar da aka yi zargin malaminta ya kashe ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending