Connect with us

Labarai

Hanifa: Ba zan bata ko da dakika daya ba wajen sanya hannu a kan hukuncin kisa – Ganduje

Published

on

Gwamna Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya tabbatar da cewa, ba zai bata ko da dakika daya ba, wajen sanya hannu kan aiwatar da hukuncin kisa ga wadanda suka yi wa Hanifa kisan gilla.

Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje ga iyalan Hanifa a Dakata Kawaji tare da mataimakinsa, Dr Nasiru Yusuf Gawuna da shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar, Labaran Abdul Madari da sauran manyan jami’an gwamnati a ranar Litinin.

Ya ce,“Zan bi dokar da kundin tsarin mulki ya tanadar a matsayina na gwamnan Kano na amincewa da hukuncin kisa a yanayin da kotu ta yanke kan masu laifin. Muna da kwakkwaran tabbaci daga kotun da ke tafiyar da lamarin cewa, za a yi adalci, ba za mu yi jinkiri ba, duk wanda aka samu da wannan danyen aiki, shima zai fuskanci kisa ba tare da bata lokaci ba. A matsayinmu na gwamnati, mun riga mun fara aikin.”

“Tsarin mulkinmu ya tanadi cewa, idan aka yanke hukuncin kisa, ikon mulki ne na gwamna ya amince a aiwatar da hukuncin kisa. Ina tabbatar muku da haka, ba zan bata koda dakika daya ba. A gaggauta gudanar da shari’a, gwamnati za ta kula da iyalan marigayiyarmu Hanifa mai albarka.” A cewar Ganduje.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending