Connect with us

Labarai

Ba za mu bari wani ya karya doka mu kyale shi ba – Lauyan Mu’azu Magaji

Published

on

Lauyan tsohon kwamishinan ayyuka Mu’azu Magaji, Barista Garzali Datti Ahmad, ya ce, tsohon Kwamishinan ya tsaya inda kuma suka cakume shi suka jefa shi a cikin motarsu suka yi gaba da shi.

Lauyansa da kuma iyalansa sun tabbatar wa BBC cewa, an kama tsohon Kwamishinan ne ranar Alhamis da daddare lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa masaukinsa bayan ya gama harkokinsa.

Ya kara da cewa,“Siyasa ce ya sanya aka turo ‘yan sanda daga jihar Kano har Abuja, domin su kama shi tun da ka ga ba shi da wani tarihi na aikata laifi.”

Ya ce, za su bibiyi lamarin da zummar daukar matakin shari’a, “Ba za mu bari wani mutum da ya ke ganin ya isa ba ya karya doka kuma a kyale shi.”

Dama dai tsohon Kwamishinan ya yi fice wajen caccakar Gwamna Ganduje, musamman bayan da tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau da wasu ‘yan majalisar dokoki sun balle daga jam’iyyar APC mai mulkin jihar suka kafa nasu tsagin da suka kira G-7.

Kazalika Mu’azu Magaji ya sha wallafa sakonni a shafinsa na Facebook inda yake cacakar gwamnatin Ganduje, wadda ya bayyana a matsayin wacce ba ta da alkibla.

A baya dai, Gwamna Ganduje, ya dakatar da tsohon Kwamishinan daga aiki bayan ya wallafa wasu sakonni da ake gani na murna ne da mutuwar Malam Abba Kyari, shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya sakamakon cutar korona.

Sai dai Mu’azu Magaji ya sha cewa ba murna ya yi da mutuwar Malam Kyari ba.

Baba Suda

NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar

Published

on

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.

 

Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.

 

A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.

Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.

Continue Reading

Labarai

Real Madrid ta kaddamar da Alexander

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta ƙaddamar da ɗan wasa Trent Alexander Arnold a yau a matsayin ɗan wasan ta

Inda shugaban ƙungiyar Flerontino Perez yace yau suna matuƙar Farin ciki kasancewar sun mallaki babban ɗan wasan baya a duniya.

 

Shima ɗan Wasa Arnold ya bayyana cewa yana cikin farin ciki kuma mafarkin sa ya cika na zama ɗan Wasan Madrid a yau.

Continue Reading

Daurin Boye

Zan shiga kawancen ‘yan jamiyyar hamayya – tsohon Minista

Published

on

Tsohon ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce a shirye yake don shiga ƙawancen ƴan jamiyyar hamayya domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027

A wata hira da BBC, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce suna ƙoƙarin samar da haɗakar siyasar da za ta samar da sauyi a ƙasar.

Amaechi wanda ɗan jam’iyyar APC ne  ya nuna damuwa kan abin da ya ƙira halin ƙuncin rayuwa da ƙasar ke ciki.

Amaechi ya ce bai cire tsammanin yin takarar shugaban ƙasa ba, illa lokaci ne kawai zai tantance.

Continue Reading

Trending