Labarai
Da Dumi-Dumi: An sauke farashin aure a Dawakin Tofa

Shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Ado Tambai ne ya tabbatar da hakana cewa, daga yanzu babu saurayin da zai yi sake kula wata budurwa, har sai ya fara tura magabatansa sun yi magana da na ta gemu da gemu, sannana kuma batun lefe an takaice shi iya akwati uku kacal.
Majalisar karamar hukumar ta Dawakin Tofa, ta aiwatar da wannan sabuwar dokar ne biyo bayan shawarwari da ta yi da masarautar Bichi, wanda a karshe aka kafa kwamiti, na musamman domin tabbatar da dokar.
a wata sanarwa da jami’in hulda dajama’a na kananan hukumomin shiyar, Sagir Abdullahi Kwanar Huguma ya sanya hannu tare da rabawa manema labarai.

Labarai
Marayu na buƙatar tallafi sosai – Kwamared Abu Saleem

Shugaban ƙungiyar tallafawa Marayu da ci gaban al’umma ta ƙaramar hukumar Birnin Kano Kwamared Adam Umar Abu Saleem, ya ce ƙarancin samun tallafi daga masu ƙarfi ne ke sanyawa Marayu ke faɗawa cikin mawuyacin hali.
Kwamared Adam Abu Saleem na wannan jawabin ne yayin zantawarsa da gidan rediyon Dala FM, lokacin musabaƙar Alƙur’ani mai girma na marayu ƴan ƙaramar hukumar Birni 5 yayin da ɗalibi dake Karkasara Ja’afar Aliyu Abubakar ya zama gwarzon shekara na ƙaramar hukumar wanda aka ɗauki nauyin al’amuran rayuwarsa baya ga kyaututtuka da ya samu, wanda Musabaƙar ta gudana cikin Firamen Salanta a ranar Asabar.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa Kwamared Adam ya ce sukan shirya Musaɓakar ne domin zaburar da Marayu akan harkokin karatun Alkur’ani mai girma, da kuma rage musu wani tunanin maraici da suke kasancewa a maban-banta lokuta.

Labarai
Lokacin zaɓe: Rundunar ƴan sanda ta shirya daƙile tayar da tarzoma – SP Kiyawa

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce, ta shirya wajen samar da tsaro, tare da ɗaukar matakin da ya dace ga ɓata garin da suke shirin tayar da tarzoma.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u a yau juma’a, yayin da yake tsokaci kan shirin da rundunar su ta yi kan zaɓe.

Labarai
Al’umma da su dage da addu’a a lokacin da za su fita zaɓen gwamna da na ƴan majalisa – Malam Ali Ɗan Abba

Gamayyar rukunin wasu Limamai da Malaman jihar Kano sun buƙaci al’umma da su dage da yin addu’a musamman ma a lokacin da zasu fita zaɓen gwamna da na ƴan majalisar jiha, domin hakan zai taimaka wajen yin zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana.
Shugaban magayyar limamai da malaman da suka fito daga Ɗariyar Tijjaniyya, Kaɗiriyya da Izala, da kuma Mahaddata Alƙur’ani mai girma na Kano Malam Ali Ɗan Abba ne ya bayyana hakan, yayin wani taron zaman lafiya da suka gudanar a ranar Alhamis.
Malam Ali Ɗan Abba, ya kuma shawarci al’umma da su gujewa tayar da tarzoma a yayin zaɓen, domin zama lafiya yafi komai mahimmanci a rayuwa.
Ya kuma ce kamata yayi suma malamai su ƙara dagewa da yin addu’in da suke yi, domin samun shugabanni na gari da za su yiwa al’umma adalci.

-
Nishadi3 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Lafiya10 months ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano