Labarai
A ci gaba da baiwa jami’an Bijilante hadin kai wajen magance tsaro – Kwamishina ‘yan sanda

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Sama’il Shu’aibu Dikko, ya ce, matukar al’umma za su ci gaba da baiwa jami’ansu dama ‘yan kungiyar Bijilante hadin kan da ya dace, babu makawa za a samu kawar da sauran bata gari.
Bayanin hakan ya fito ne ta bakin baturen ‘yan sandan yankin Sharada SP Abdulrrahim Adamu, wanda ya wakilci kwamishinan a yayin taron yaye
dalibai 700 da kungiyar daliban Sharada (SHASA) da ta koyawa sana’o in dogaro da kai, wanda ya gudana cikin wani dakin taro dake kan titin
Yahya Gusau a yau Lahadi.
SP Abdulrrahim ya kuma kara da cewar, masu yin amfani da shafukan sada zumunta su kaucewa yin amfani da wayoyinsu a kan hanya, domin
gudun fadawa komar bata gari.

Kayan sana’o’in da matasa suka koya
Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar Kwamared Bukhari Isah Sa’ed, ya ce, sun koyawa matasan sana’o in ne domin su dogara da kansu, inda
ya kumayi kira ga matasa.
A yayin taron dai al’umma da dama ne dai suka samu damar halarta kuma ciki akwai shugaban kungiyar kare hakkin dan adam ta Global Community for Human Right Network Kwamared Karibu Yahya Lawan Kabara, harma da Dagacin Sharada Alhaji Ilyasu Mu’azu Sharada.

Labarai
Matashin da ke Sansana bayan Akuya yana sakawa a TikTok ya shiga hannun hukumar Hisbah a Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wani Matashi da aka yi zargin ya sansana bayan wata Akuya, a matsayin yana son ya yi suna a shafukan sada zumunta.
Mataimakin babban kwamandan hukumar Hisbah Dakta Mujahideen Aminudeen Abubakar, ya shaidawa Dala FM Kano cewar, sun kama matashin ne mai suna Shamsu Yakubu dan garin Dawakin kudu, mai shekaru 24, bayan da dagacin garinsu ya kawo korafi akansa.
Dagacin ya ce an kai ƙorafin matashin ne saboda yadda mutanen garin suka yi kokarin farmasa, bayan da aka gano bidiyonsa a shafin TikTok yana sansana bayan Akuya.
Yanzu haka hukumar ta ɗauki matakin kai matashin a fara yi masa gwajin Ƙwaƙwalwa, da kuma na ta’ammali da kayan maye.

Labarai
Kisan gillar Edo: A gaggauta nemawa mutanen da aka kashe haƙƙin su, ko mu ɗauki Mataki bisa doka – Human Rights

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network, ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta Kano da kuma ta jihar Edo, da gaggauta neman haƙƙin Mafarautan nan ƴan asalin jihar Kano waɗanda aka yi wa kisan gilla a garin Uromi na jihar Edo.
Daraktan ƙungiyar na ƙasa Kwamared Gambo Madaki shi ne ya bayyana wa tashar Dala FM Kano, hakan a ranar Litinin, lokacin da yake tsokaci kan kisan sama da Mafarauta 16 a jihar Edo, waɗanda suka taho daga jihar Ribas za su dawo gida Kano.
Ya ce baya ga ɗaukar matakin lalubo waɗanda suka aikata rashin imanin, akwai buƙatar a ɗauki mummunan mataki akan su don daƙile afkuwar irin hakan a gaba.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu ɓatabgari ne su ka damke wadanda abin ya shafa a Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas ta Jihar Edo, inda su ka ga bindigogin farauta, sai kawai su ka yanke cewa ai masu garkuwa da mutane ne, inda suka kona su da ransu a ranar Alhamis.
Lamarin dai ya jawo cece-ku-ce, inda ‘yan Najeriya da dama ke zargin gwamnati da gazawa wajen dakile irin wannan ɗaukar doka a hannu.
A cewar Gambo Madaki, baya ga batun kafa kwamiti da gwamnatin Kano ta yi akan wannan batun, ya kamata gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙara bibiyar lamarin da kan sa, don ganin an ɗauki matakin da ya dace akan kisan gillar ko kuma su ɗauki mataki bisa doka.

Labarai
Mun baza jami’an mu lungu da saƙo don samar da tsaro yayin bikin Sallah a Kano – Anty Snaching Phone

Rundunar tsaron nan da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Waya da kuma dakile Shaye-shayen kayan maye, ta Anty Snaching Phone, ta ce ta baza jami’an ta kusan dubu ɗaya da za su shiga lungu da saƙo na jihar nan, domin samar da tsaro a yayin bukukuwan ƙaramar Sallah.
Kwamandan rundunar a nan Kano Inuwa Salisu Sharaɗa ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Freedom Radio, ya kuma ce jami’an su za su yi duk mai yiyuwa wajen daƙile ayyukan ɓata garin da ke shirin tayar da hankalin al’umma yayin bikin sallar.
“Daga cikin jami’an mu da za su samar da tsaron akwai na cikin kayan mu da kuma na farin kaya, kuma sun fara bazama guraren da mu ka tura su tun cikin kin daren Asabar ɗin nan kuma za su yi aiki cikin ƙwarewa kamar yadda suka samu horo, “in ji Inuwa”.
Sharaɗa, ya kuma ce hakan na cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano ƙarkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa kulawar shugaban kwamitin karta-kwana da ke yaƙi da miyagun ɗabi’u da gwamnan ya kafa ƙarkashin Dakta Yusuf Ƙofar Mata.
Wannan dai na zuwa ne yayin da za’a gudanar da sallar Idi, ta ƙaramar Sallah a ranar Lahadin nan a Najeriya, da Jamhuriyyar Nijar da ƙasar Saudiyya, da ma wasu ƙasashen Duniya.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su