Connect with us

Labarai

Da Dumi-Dumi: Dan Sarauniya zai zauna a gidan ajiya da gyaran hali har sai 3 ga watan gobe – Kotu

Published

on

Kotun Majistret mai lamba 58 karkashin jagorancin mai shari’a, Aminu Gabari, ta aike da tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Injiniya Mu’azu Magaji gidan ajiya da gyaran hali har zuwa nan da watan Fabrairu.

wakilin mu na Kotu, Yusuf Nadabo Isma’il, ya rawaito cewa, za a dawo zaman kotun a ranar 3 ga watan Fabrairu, domin sanin ko za a bayar da Dan Sarauniya a hannun belo ko kuwa.

A na  dai tuhumar Injiniya Mu’azu Magaji Dan Sarauniya bisa zargin bata suna da cin mutuncin Gwamnan Kano da iyalan sa.

Kunshin tuhumar ya bayyana cewar, wani lauya ne mai suna, Adekunle Taiwo, ya shigar da kara a madadin gwamnan Kano a kan cewar, Dan Sarauniyar ya sanya wani hoto a shafinsa na Facebook wanda kuma sanya wannan hoto cin mutunci ne ga gwamnan Kano Ganduje.

Yayin da aka karanta masa tuhumar ya musanta dukkanin tuhume-tuhumen da a ke yi masa.

Lauya mai gabatar da kara, Wada A Wada ya roki kotun da ta sanya wata ranar dan su gabatar da shaida.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa, Barista Garzali Datti Ahmad, shi ne lauyan wanda ake tuhuma ya roki kotun da ta sanya Dan Sarauniyar a hannun beli ya kuma tallafi rokon da sashi na 35 da na 36 (5) na kundin tsarin mulkin kasa, ya kuma tallafi rokon da sashi na 168 da na 172 da kuma sashi na 172 na kundin tafikar da shari’ar ACJL 2019.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending