Connect with us

Manyan Labarai

Yanzu-Yanzu: Senegal ta dauki kofin nahiyar Afrika

Published

on

Ƙasar Senegal ta zama zakara a gasar cin kofin nahiyar Afrika a karo na farko bayan ta doke Masar da ci 4-2.

Senegal ta samu nasara a bugun daga kai sai mai tsaron raga, bayan da a ka shafe mintuna 120 a na fafatawa a tsakanin juna.

Mai tsaron ragar Senegal Mendy wanda ya samu kyautar gwarzon ɗan wasan Afrika, ya buge ƙwallo biyu, bayan da ɗan wasan Masar ya buga ɗaya jikin tirke, shi kuwa Gabaski wanda ya samu kyautar gwarzon ɗan wasa a wasan da a ka fafata, ya buge ƙwallon ɗaya.

Manyan Labarai

Lauya ya nemi a biya Abduljabbar Kabara Naira miliyan 20 saboda ɓata masa lokaci da aka yi.

Published

on

Babbar kotun jaha a ɓangaren ɗaukaka ƙara ƙarƙashin masu Shari’a Aisha Mahamud, da Nasir Saminu, sun sanya ranar 9 ga wannan watan da ake ciki dan ci gaba da sauraron daukaka karar, da Abduljabbar Nasir Kabara ya shigar.

A zaman kotun na yau lauyan Abduljabbar, Barrista Yusuf Sadik, ya shaidawa kotun cewar a shirye suke a fara sauraron daukaka karar.

Sai dai lauyan gwamnati ya bayyana cewar basu shirya ba dan haka a sanya wata ranar.

Lauyan Abduljabbar ya shaidawa kotun cewar sun bai wa lauyoyin gwamnati takardun bayaninsu tun a watan 2 da ya gabata, dan haka a biya Abduljabbarun Naira miliyan 20 saboda ɓata masa lokaci da aka yi.

Sai dai lauyan gwamnati ya yi suka an kuma duba lokacin da aka bada takardun a watan uku ne dan haka wannan lauya ya janye rokonsa.

Daga nan ne kotun ta sanya ranar 9 ga watan nan na Mayu da ake ciki, an kuma umarci lauyan gwamnati da ya yi martani idan yana da shi kafin wannnan rana.

Wakilinmu na Kotu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa, Abduljabbar Nasir Kabara dai ya daukaka karar ne dan kalubalantar hukuncin kutun shari’ar muslunci ta kofar kudu, wadda ta yanke masa hukuncin kisa ta hanya rataya bisa samunsa da laifin ɓatanci.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gobara ta ƙone tarin kayayyaki a gidan tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau

Published

on

Wata Gobara ta tashi a Gidan Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau dake Mudubawa a yankin Karamar hukumar Nassarawa, inda ta ƙone wasu kayayyaki a ɗakin matar sa waɗanda zuwa yanzu ba’a ƙayyade ba.

Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta faro ne daga ɗakin Girki na matar tsohon gwamnan Hajiya Halima Shekarau, tun yammacin jiya Lahadi.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, mai magana da yawun tsohon Gwamnan Malam Sule Ya’u Sule, ya ce gobarar ta shafi iya daki ɗaya ne a cikin gidan dake Munduɓawa.

A nasa ɓangaren kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, PFS Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce da zarar sun kammala tattara alƙaluma da bincike, zai magantu a nan gaba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnan Kano ya ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa ta Ɗan Agundi

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa da za’ayi a mahaɗar Ɗan Agundi, da ke ƙaramar hukumar Birni, domin samarwa al’ummar jihar saukin zirga-zirga a yankin.

Da yake ƙaddamar da aikin a yammacin yau gwamnan ya ce, gwamnatin Kano za ta sanya idanu wajen ganin an kammala aikin cikin ƙanƙanen lokaci, hakan yasa yanzu gwamnatin ta tanadi duk wasu kayan aiki da ake buƙata domin gudanar da aikin cikin nasara.

Har ila yau, gwamnan Abba Kabir, ya kuma ce an samar da hanyoyin da al’umma za su bi, domin samun saukin zirga-zirga har zuwa lokacin da za’a kammala aikin baki ɗaya.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce, an samo kanfani mai inganci wanda zai yi aikin cikin ƙanƙanen lokaci, domin ci gaba da gudanar da zirga-zirga akan lokaci.

Continue Reading

Trending