Connect with us

Kimiya

Rahoto: Fasahar Matasa na Cigaba da Habaka a Kano

Published

on

Rahoto: Fasahar Matasa na Cigaba da Habaka a Kano

 

Fasaha da kere-kere tsakanin matasa abune da ya zama ruwna dare a tsakanin matasa a jihar Kano, inda zakaga matasa na kera motoci, gidaje na gwangwani da kuma kwali ko na katako.

Shin ko wane tallafi wadannan matasa dake wannan kere-keren ke samu?

Wane irin kalubale suke fuskanta?

Akan wannan batune wakilinmu Abdulbasid Abdulmumin ya hada mana rahoto akai.

Saurari Rahoton ko Kuma Saukewa akan Wayarka

 

Hotuna:

Ayi sauraro lfy.

Baba Suda

Ƴan Nigeria miliyan 20 ne ke da taɓin-hankali – WHO

Published

on

Wani rahoto da hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta fitar ya ce ƴan Najeriya miliyan 20, daidai da kashi 20 cikin 100 na al’ummar kasar, na fama da matsalar taɓin-hankali.

 

Dr Azubike Aliche, Sakataren Kwamitin Amintattu na Cibiyar Kula da Lafiyar Ƙwaƙwalwa ta Najeriya-Amurka (NAIMH) ne ya bayyana haka a wani shirin horo kan lafiyar kwakwalwa da GAP Action da cibiyar su ka shirya a Owerri a jiya Talata.

 

Ya bayyana cewa “lamarin mai tayar da hankali ne” game da ciwon damuwa da ƴan Nijeriya ke fama da shi, wanda ya ce, ya kasance mafi girma a duniya kuma ya yi kira da a yi ƙoƙari matuƙa don canza yanayin.

 

“Rahotanni da ake samu sun nuna cewa kashi 10 cikin 100 na masu fama da tabin hankali ne kawai ke samun kulawa a Najeriya kuma dole ne a canza wannan yanayi,” in ji shi.

 

 

 

TRT Hausa

 

 

 

 

Continue Reading

Baba Suda

Dumamar yanayi :- Gwamna Zulum ya haramta sare bishiyu

Published

on

Gwamnan jihar Borno Baba Gana Umar Zulum ya kaddamar da wasu dokokin biyu ga al’ummar Jihar.

Dokar farko itace Gwamnan ya haramta sare bishiyu a dukkanin fadin jihar, Inda kuma ya Kara kaddamar da dokar tsaftace muhalli a dukkanin karshen wata.

 

Yayin da yake kaddamar da dokar Gwamna Zulum yace duba da dumamar yanayi da ake fuskanta a yanzu gwamnati ta haramta sare bishiyu a fadin jihar Borno.

Haka kuma saboda Kare lafiya da kuma al’ummar Jihar dole ne dukkanin karshen wata a gudanar da tsaftar muhalli a Jihar Borno.

 

” A matsayi na Wanda kundin tsarin mulkin kasa ya bani dama, ni Baba Gana Umara Zulum na haramta sare bishiyu a fadin jihar Borno, kuma na saka dokar wajibi ne kowa ne dan Jihar ya tsaftace muhalli a dukkanin karshen wata, saboda inganta lafiyar al’ummar Jihar Borno.”

Continue Reading

Kimiya

SIKILA – Ko ka San matsalolin Ƙwayar Jini Mai Sikila?

Published

on

Shafin Physiotherapy Hausa ya bayyana cewa Ciwon sikila ko kuma amosanin jini, wato ‘Sickle Cell Disease’ a turance, ciwon jar ƙwayar halittar jini ne da ake gadar sa daga iyaye (mace da namiji). Lafiyayyiyar jar ƙwayar jini tana da sifar da’ira ne. Amma masu ciwon sikila, jar ƙwayar jininsu tana zama sifar lauje ko baka ne, wato ‘sickle’ a turance.

A yayin da mafi yawan sifar jar ƙwayar jini ta zama sifar lauje a ciki jini:

1] Wannan zai rage wa jar ƙwayar jinin ikon shaƙar wadatacciyar iskar oksijin daga huhu domin kaiwa zuwa sassan jiki.

2] Saurin tafiyar ƙwayar jinin a cikin jijiyoyin jini zai ragu.

3] Harɗewa ko sarƙewar jajayen ƙwayoyin jini yayin da suke gogayya a ƙoƙarin shiga siraran jijiyoyin jini.

4] Fashewa ko mutuwar ƙwayoyin jini kafin cikar wa’adin kwanaki 115 zuwa 120 da ya kamata su yi suna aiki a jiki.

Daga cikin matsalolin da masu ciwon sikila ke fuskanta akwai:

1. ƙamfar jini, wato ƙarancin jini a jiki, sakamakon yawan fashewar ƙwayoyin jinin kafin cikar wa’adinsu.

2. Kumburin fuska, tafukan hannu da sawu.

3. Jinkirin girman jiki da tsaikon balaga.

2. Matsanancin ciwon jiki da gaɓɓai.

4. Sauri ko yawan harbuwa da ƙwayoyin cutuka da ke kama ƙashi da gaɓoɓi.

5. Lalacewar ƙashi da ruɓewar sassan jiki da dai sauransu.

Likitocin fisiyo na ba da gudunmowa ga masu ciwon sikila yayin da suka gamu da matsalolin da ke tattare da ciwon sikila kamar: matsanancin ciwon jiki da gaɓoɓi, riƙewar gaɓoɓi, raunin ko rashin ƙwarin tsokokin jiki, dashen gaɓar ƙugu, dashen gaɓar gwiwa, yanke sassan jiki, jinkirin matakan girman yaro da dai sauransu.

Muradin likitan fisiyo ga mai ciwon sikila shi ne samun rayuwa cike da aiki cikin kuzari da karsashi ba tare da ciwo ko nakasa ba.

MATAKIN KARIYA

Daga ƙarshe, ana iya kauce wa haɗarin haifar yaro mai ciwon sikila ta hanyar yin gwajin ‘genotype’ ga ma’aurata kafin aure domin gano yiwuwa ko akasin haifar yaro mai sikila.

Tabbata ka san gwajin ‘genotype’ ɗinka da na wace za ka aura domin tabbatar da cewa ba ku da haɗarin haifar yaro mai ciwon sikila.

Continue Reading

Trending