Connect with us

Labarai

Kannywood: Maishadda ya musanta batun auren sa da Aisha Humaira

Published

on

Fitaccen mashiryin fina-finan masana’antar Kannywood, Bashir Maishadda, ya musanta labarin dake ta karadewa a shafukan sada zumunta cewa, zai auri jaruma Aisha Humaira, biyo bayan ganin su da a ka yi tare a wani hoto.

A zantawarsa da Dala FM, ya ce, sun dauki hoton ne kawai, saboda tallata kayan wani kamfani, mutane kuma suka ara suka yafa, suna cewa wai budurwarsa ce, kuma auren ta zai yi.

Ya kuma ce, ko kusa ko alama ba maganar aure a tsakanin su da ita, kawai dai aiki ne ya hada su.

Har yanzu dai dai hoton Bashir Maishadda da Aisha Humaira na ci gaba da daukar hankali a shafukan na sada zumunta da sunan cewa, wai aure za su yi, in banda a wannan lokaci da ya karyata.

Labarai

Maulidin Inyass: Har yanzu babu wata matsalar tsaro da aka fuskanta a Kano – Anty Snaching Force

Published

on

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Waya da kuma daƙile Shaye-shayen kayan maye ta Anty Snaching Force a Kano, ta ce kawo yammacin yau Asabar babu wata matsalar tsaro da aka samu a faɗin jihar, saɓanin wani rahoto da aka rinƙa yaɗawa a ranar Juma’a, cewar za’a iya fuskantar hakan.

Kwamandan rundunar, kuma mashawarci na musamman ga gwamnan Kano akan tsaro Inuwa Salisu Sharaɗa, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da tashar Dala FM Kano, a yammacin yau Asabar 25-01-2025.

Wannan dai na zuwa ne a wani ɓangare na Maulidin Shehu Ibrahim Inyass da aka gudanar karo na 39, ranar Asabar a filin wasa na Sani Abacha Stadium da ke jihar Kano, wanda al’umma da dama daga sassan jahohihin Najeriya, da ma wasu ƙasashe suka halarta.

“Tun kafin a fara gudanar da maulidin Shehu Ibrahim Inyass, da lokacin gudanarwa har zuwa kammalawa, jami’an mu suka rinƙa zirga-zirga a cikin ƙwaryar birnin Kano, amma har zuwa yammacin yau ɗin nan ba mu samu wata matsala ta tsaro ba, “in ji Inuwa”.

A cewar sa, a zagayen da suka fara tun daga cikin daren jiya a ƙoƙarin su na daƙile matsalar tsaro yayin maulidin, sun kwana muna zirga-zirga a birnin Kano, tare da ziyartar irin su unguwannin Zango, da Hasiya Bayero, da Ƙofar Mata, da kuma gidan Murtala, da dai sauransu yankuna, baya ga zuba jami’an mu da muka yi a filin wasan na Sani Abacha Stadium.

Kwamandan rundunar tsaron ta Anty Snaching Force Inuwa Salisu, ya kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da basu haɗin kai domin ganin an ƙara magance matsalolin tsaro a faɗin jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.

Daga cikin manyan baƙin da suka samu damar halartar taron Maulidin akwai Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa, da mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, da Malamai, da ƴan Siyasa, da sauran al’umma.

Continue Reading

Labarai

Rashin bayar da shawarwari na kawo tsaiko a karatun Ɗaliban Najeriya – Farfesa Abdurrasheed Garba

Published

on

Shugaban jam’i’ar Khalifa Isyaka Rabi’u ta Chairun da ke jihar Kano Farfesa Abdrulrahsheed Garba, ya ce rashin shigar da tsarin jagoranci da bada shawarwari a mafi yawa daga cikin makarantu a Nijeriya, na taimaka wa wajen sanya matasa su gaza hawa kan kyakkyawar turbar da ta dace da su a rayuwar karatun su da ma sauran al’amura daban-daban.

Farfesa Abdrulrahsheed Garba ya bayyana hakan ne a ganawar sa da gidan rediyon Dala FM, yayin wata ziyara ya da ya kawo gidan a yammacin Juma’a 27 ga watan Disamban 2024.

“Tun kusan shekaru hamsin aka sanya jagorancin da bada shawarwarin wato Guiding and Cancelling, a cikin tsarin ilmin ƙasa a Najeriya, sai dai har kawo yanzu da yawa daga cikin gwamnatocin jahohi da ma gwamnatin tarayya sun gaza tabbatar da shi, “in ji shi”.

Farfesa Abdrulrahsheed Garba, ya kuma ƙara da cewa akwai buƙatar iyaye da makarantu su ƙara dagewa akan ƴaƴan, ita kuma gwamnati ta kara samar da ingantattun makarantu, domin ganin rayuwar ɗalibai ta ƙara hawa kan turba mai kyau.

Continue Reading

Labarai

Ƙarancin kayan aiki na bamu matsala wajen kakkaɓe masu faɗan Daba da ƙwacen Waya a Kano – Anty Snaching Phone

Published

on

Rundunar tsaron nan mai yaki da fadan Daba da ƙwacen Waya da kawar da Shaye-shaye ta Anty Snaching da ke jihar Kano, ta sha alwashin ci gaba da kakkabe bata garin da ke addabar al’umma da fadan Daba a sassan jihar, domin ƙara wanzuwar zaman lafiya a fadin jihar.

Kwamandan rundunar Inuwa Salisu Sharada, shi ne ya bayyana hakan a zantawarsa da gidan redivon Dala FM, a ranar Litinin.

Ya ce za su ci gaba da kokari wajen shiga lungu da sako wajen kawar da dukkanin masu kokarin tayar da hankalin al’umma, duk kuwa da ƙalubalen da suke fuskanta.

“Daga cikin ƙalubalen da muke fuskanta akwai ƙarancin motar fita aiki domin mota ɗaya muke da ita, idan jami’an mu za su fita aiki da mutane da yawa sai dai su hau Baburan Adai-dai Sahu, duk hatsarin wuri; akwai mota a gidan gwamnatin Kano muna fatan gwamna zai bamu ita a ciki gaba da aiki, “in ji Inuwa”.

Kazalika Sharada ya kuma ƙara da cewa akwai buƙatar al’umma su ƙara himma wajen ba su hadin kan da ya dace domin ganin sun kara samun dama wajen magance matsalar tsaro musamman ma ta fadace-fadacen Daba, da ta addabi al’umma a sassan jihar Kano.

A cewar sa, “Ƙarancin motocin fita aikin na ba mu matsala domin a wasu lokutan daga wuri mai nisa ake kiran mu don kai ɗauki akan matsalar tsaro, amma rashin wadatattun motocin mukan fuskanci ƙalubale, “in ji shi”.

Wannan dai na zuwa ne yayin da al’umma ke a gaba da neman dauki wajen magance matsalar tsaron da ke damun su a sassan jihar, musamman ma a wasu unguwanni da ke ƙwaryar bimin Kano.

Continue Reading

Trending