Ƙasashen Ƙetare
Kishin Kasa: Tsohon sojan Ukraine ya nufi gida domin taimakawa kasar sa
A yayin da ‘yan gudun hijirar Ukraine ke ci gaba da tururuwa zuwa mashigar kan iyaka, domin gujewa mamayar Rasha, shi kuwa wani tsohon sojan yaki, Dmytro Dovzhenko, ya nufi wata hanya ta daban daga kasar Poland, domin komawa rundunarsa ta soja.
Dan shekaru 40, wanda ya yi yaki a Donbass a shekarar 2014, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Juma’a cewa, ya bar matarsa da ‘ya’yansa biyu, kuma ya na cikin wasu tsofin sojan Ukraine kusan 700.
Dovzhenko ya ce, “Iyalina ba su yi farin ciki da barina ba,” in ji Dovzhenko, sanye da gajiyar aikin soja da kuma wata babban zoben sa hannu da aka rubuta “Loyal Forever” daga rundunarsa ta ruwa a Ukraine.
“Ina fatan dawowa gidana, idan ban dawo ba, ina fatan komai zai daidaita.” in ji Tsohon sojan.
Kasar Rasha dai ta kaddamar da wani farmaki na bai daya a kan kasar Ukraine ta kasa da sama da kuma ta ruwa. Dubban ‘yan kasar Ukraine ne suka fara isa kasashen tsakiyar Turai makwabta. da Poland sun komawa gida domin gwabzawa da Rasha.
Ƙasashen Ƙetare
Sojoji Sun yi juyin Mulki a Gabon
Sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon tare da sanar da karbi mulki.
Sun ce sun soke sakamakon zaben da ka gudanar ranar Asabar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.
Hukumar zaben ta ce Mr Bongo ya samu nasara ne da kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.
Sun Kuma ce Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalan gidansu ke yi a Gabon.
Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin dake sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa dukkan hukumomin kasar.
Daya daga cikin sojojin ya fada a tashar talabijin ta Gabon 24 cewa, “Mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ake yi a yanzu.”
Mr Bongo ya hau karagar mulki lokacin da mahaifinsa Omar ya rasu a shekara ta 2009.
Ƙasashen Ƙetare
Sojoji sunyi juyin Mulki a jamhuriyar Nijar
Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa Sojojin Kasar sun yi juyin Mulki, tare da sanar da kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum.
Cikin sanarwar da suka bayar a gidan telebijin din Kasar, jagoran tawagar sojojin Kanal Amadu Abdramane yace “mun kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum tare da karbe dukkanin Wani Iko”.
Sojojin dai sun bayar da dalilin halin rashin tabbas da Kuma Matsin tattalin arziki a kasar.
Tuni dai sojojin suka garkame dukkanin iyakokin Kasar tare da Sanya dokar takaita zirga zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.
Tun a safiyar laraba ne dai aka wayi gari da fara wancan yunkuri, Wanda yanzu haka ta tabbata, Kasar Nijar na hannun sojoji, Wanda shi ne Karo na hudu ana gudanar da juyin mulkin a jamhuriyar Nijar.
Ƙasashen Ƙetare
An tsaurara tsaro a fadar shugaban Kasar Nijar
Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar, na nuni da cewa dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasa sun rufe duk wata hanyar shiga fadar a wani lamari da ba a kai ga ganowa ba.
Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasar ta Nijar na tattaunawa da sojojin domin sasanta lamarin.
Karin bayani nan tafe….
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su