Connect with us

Labarai

Mai kwacen waya a Adaidaita ya sake shiga hannun KAROTA karo na 2

Published

on

dan KAROTA ya rasa ransa abakin aiki

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano KAROTA, ta ƙara cafke matashi Abdullahi Babakura, wanda a ka kama shi makwanni biyu da suka gabata da zargin yin amfani da Baburin Adaidaita Sahu ya na satar wayoyin jama’a.

An kama Babakura ne a kan titin Kundila Maiduguri Road, lokacin da wani matashi mai suna Abdulhadi Isyaku ya buƙaci Babakura ya kai shi kan titin Kano Gest-in.

Bayan da suka ɗauke masa waya sai suka ce masa ba inda ya buƙata za su je ba, kamar yadda Abdulhadi ya shaidawa Hukumar KAROTA. A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa.

Maƙwanni biyu da suka gabata, Hukumar KAROTA ta cafke Abdullahi Babakura da aikata makamancin laifi irin wannan, inda a ka miƙa shi a hannun ƴan sanda domin faɗaɗa bincike.

A binciken da KAROTA ta gudanar ta gano cewa, bayan da ƴansanda suka gudanar da binciken sun gabatar da shi a gaban Kotu, inda ta yanke masa hukuncin zaman gidan gyaran hali ko zaɓin biyan tara.

Bayan ya biya tarar ne ya fito domin ci gaba da aikata makamancin laifin.

Babakura ya bayyana cewa ba shi kaɗai yake yin satar wayar ba suna yi ne tare da wani abokinsa mai suna Abbati Bright a inda da zarar sun ɗauki wayar Fasinja sai su ce ba inda ya buƙata za su je ba.

Hukumar KAROTA ta miƙa Abdullahi Babakura Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar ƴan sandan jihar Kano domin faɗaɗa bincike.

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Labarai

Dilolin Wiwi sun yanki mai unguwa da Wuƙa, tare da cizon shi a hannu, kan ya shana su sha da siyar da wiwi a Kano

Published

on

Wasu matasa da ake zargin ƴan Daba ne, kuma dilolin Wiwi, sun kai wa mai unguwar yankin Bachirawar Tukwane ƙarshen kwalta hari da muggan makamai.

Tun farko dai mai unguwar yankin Malam Mustapha ya shawarci matasan ne, da su dai na ɗaurin tabar Wiwi, da siyar wa a kofar gidajen mutane lamarin da ya tunzura matasan.

Matasan dai sun rutsa mai unguwar Bachirawar ne inda suka yi yunƙurin hallaka shi, bayan da suka yanke shi da Wuƙa, tare da cizon sa a Hannu, sai dai ‘yan ƙungiyar bijilante na yankin sun kawo masa ɗauki inda suka kama wani matashi mai laƙabin Kokuwa.

A lokacin ne kuma mutanen yankin suka yi yunƙurin ɗaukar doka a hannu, sai dai mai unguwar Bachirawa Malam Mustapha dan Bachirawa Gabas Malam Abdulkadir Dandiyo, sun kuɓutar da matashin inda aka mika shi ofishin ƴan sanda, ragowar matasan suka tsere.

Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar yankin Dakta Jibrin Sagir, ya ce a shirye suke su tinkari duk wani ɓata gari a yankin da yake addabar su.

Continue Reading

Trending