Connect with us

Labarai

Kotu ta daure magoyin bayan Everton tare da hana shi shiga kallo na wata 12

Published

on

Wani mai goyon bayan Everton da ya jefa kwalbar da ta bugi dan wasan Aston Villa, Matty Cash, an yanke masa hukuncin dakatar da shi shiga wasan kungiyar na tsawon shekaru hudu tare tura shi gidan yari.

An kuma bai wa Roger Tweedle hidima na sa’o’i 100 domin ya yi wa al’umma aiki, bayan ya jefa kwalbar zuwa filin wasa a Goodison Park a watan Janairu, wanda Villa ta ci 1-0.

Al’amarin ya faru ne daf da tsakar rana a lokacin da ‘yan wasan Villa suka yi murnar cin kwallon da Emi Buendia ya bugo da kai, wanda hakan ya zama ci daya tilo a wasan.

Everton ta tabbatar jim kadan bayan kammala wasan cewa ta gano wanda ya yi jifan, uma ‘yan sandan Merseyside ne ke gudanar da lamarin.

Matashin mai shekaru 19 ya amsa laifinsa a ranar Litinin a Kotun Majistare bisa cin zarafi da ya yi wa Cash, kuma an yanke masa hukuncin daurin makonni takwas a gidan yari, kuma an dakatar da shi na tsawon watanni 12.

An kuma umarce shi da ya biya tarar Fam 200, da kuma Fam 85 na farashi da Fam 128 ga wani asusu na wadanda aka yi wa laifi.

Labarai

Ƙudurin gyaran dokar gudanarwar Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi ya tsallake karatu na ɗaya a majalisar dokokin Kano

Published

on

Ƙudurin gyaran dokar gudanarwar Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke jihar Kano, ya tsallake karatu na ɗaya a zauren majalisar dokokin jihar.

Ƙudurin ya kai wannan mataki ne yayin zaman majalisar na yau Laraba, ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore, bayan da akawun majalisar Alhaji Bashir Idris Ɗiso, ya gabatar da karatun na ɗaya.

Har ila yau, yayin zaman na yau, majalisar ta buƙaci gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ta tallafa wa wasu kanikawa da kafintoci bisa iftila’in gobarar da ta ƙone musu kaya na miliyoyin Naira, tare da asarar rayuka a kan titin Lawan Dambazau.

Majalisar ta buƙaci hakan ne biyo bayan ƙudurin gaggawa da wakilin ƙaramar hukumar Birni da kewaye Alhaji Sarki Aliyu Daneji ya gabatar.

Yayin gabatar da ƙuɗurin, ɗan majalisar ya nemi gwamnatin data tallafa wa waɗanda gobarar ta shafa domin rage musu raɗaɗin iftila’in.

Majalisar ta kuma bukaci gwamnatin da ta ɗaga darajar asibitin garin Gano, zuwa matakin babban asibiti domin ƙara inganta kiwon lafiya a yankin har ma da sauran yankuna, kamar yadda ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Shu’aibu Rabi’u ya buƙata.

Wakilinmu na majalisar Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito cewa, a dai zaman na yau Laraba, shi ma ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ƙaraye, Injiniya Ahmed Ibrahim, ya gabatar da ƙudurin neman gwamnatin Kano ta gina titi a hanyar da ta tashi daga mahaɗar titin zuwa sansanin horas da matasa ƴan hidimar ƙasa, ta bi ta Kurugu da Dederi har zuwa Yammedi duk a yankin ƙaramar hukumar Ƙaraye.

Continue Reading

Labarai

Gwamnan kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sauya shugaban hukumar tattara haraji na jihar

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗin Dakta Zaid Abubakar, a matsayin sabon shugaban hukumar tattara kuɗaɗen haraji ta jihar Kano, da kuma Kasim Ibrahim a matsayin babban daraktan hukumar.

Babban daraktan yaɗa labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar da aka aikowa Dala FM Kano, a daren jiya Laraba.

Sanarwar ta ce, tsohon shugaban hukumar Alhaji Sani Abdulkadir Dambo, an mayar da shi ne a matsayin mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin zuba jari, wanda kuma sauye-sauyen za su fara aiki nan take.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur: Fadar shugaban ƙasa kiyi wani abu dan mutane su samu sauƙi – Ƙungiyar Nothern Concern Soliderity

Published

on

Yayin da al’umma ke ci gaba da fuskantar wahalar man fetur a ƙasar nan, ƙungiyar da ta damu da abubuwan da suka shafi arewacin ƙasar nan ta Northern Concern Soliderity, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi abinda ya dace dan ganin mutane sun samu wani sauƙi.

Babban jami’in gudanarwar ƙungiyar, kuma sakataren riƙo na zauren gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya, Kwamared Saddat Usman Maiyaƙi, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, lokacin da yake nuna takaici kan irin wahalar da al’ummar ƙasa suke sha wajen shan man Fetur a gidajen man.

Ya ce duba da halin matsin rayuwar da al’umma suka samu kansu a ciki, akwai buƙatar shugabanni da masu ruwa da tsaki su kawo ƙarshen wahalar man Fetur ɗin da aka fama da ita.

Kwamared Saddat Maiyaƙi, ya kuma haƙurƙurtar da al’ummar ƙasar nan kan halin ƙuncin rayuwar da suka samu kai a ciki, inda ya yi fatan komai ya zo karshe cikin ƙanƙanen lokaci.

Continue Reading

Trending