Connect with us

Labarai

Kungiyar yardaddun matan Kwankwasiyya sun gwangwaje marasa karfi da kayan abinci

Published

on

Sakatariyar Ƙungiyar Yardaddun matan Kwankwasiyya, Hauwa Bello Fulani, ta ce kamata ya yi matan gida su fito a rinƙa damawa da su, wajen tallafawa masu ƙaramin ƙarfi musamman ma a wannan wata na Ramadan da muke ciki.

Hauwa Fulani ta bayyana hakan ne a zantawarta da Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u, lokacin da ƙungiyarsu ta raba tallafin kayayyakin abinci da na shan ruwa, ga iyayen marayu aƙalla su 183, wanda suka zagaya ƙaramar hukumar Tarauni, Kumbotso, da dai wasu ƙananan hukumomin Kano, domin rage musu wata damuwa da take damunsu, a ranar Lahadin nan.

“Da ɗari da kwabo muke tara kuɗaɗen da muke siyan kayayyakin abinci da na shan ruwa a junan mu matan ƙungiya, domin tallafawa marayu da iyayensu a kananan hukumomin Kano, ba tare da samun tallafi daga ko ina ba, “inji Hauwa Fulani.

Labarai

Ba mu san Hamisu Breaker ya saki waƙar Amanata ba – Hukumar tace fina-finai

Published

on

Hukumar tace Fina-finai da Ɗab’i ta jihar Kano ta ce yanzu haka tana kan bincike don gano yadda akai mawakin nan Hamisu Breaker, ya saki sabuwar wakarsa mai suna “Amanata” ba tare da an tantance ta ba.

Mai magana da yawun hukumar Abdullahi Sani Sulaiman, shi ne ya bayyana hakan a wani sakon murya da ya aikowa Dala FM Kano, a ranar Alhamis 24 ga watan Afrilun 2025.

Ya kuma ce aikin dakatar da wakar ba na hukumar Hisbah ba ne na hukumar tace fina-finai ne, amma ba laifi ba ne kasancewar duk hukumomi ne na Gwamnati, a don haka idan hukumar ta Hisbah ta magantu akai babu laifi, domin dama suna aiki kafaɗa da kafaɗa.

A game da wakar ta Hamisu Beraker, mai suna “Amanata”, Abdullahi Sani, ya ce su har yanzu ba su san ta ina wakar ta fita ba tare da an tantance ta ba, amma tuni shugaban hukumar Abba Al-mustapha ya bada umarnin gudanar da bincike akan ta.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ce dai ta hannun mataimakiyar babban kwamandan ta a ɓangaren mata Dakta Khadijah Sagir Sulaiman, ta yi Allah wa-dai da wakar Hausar mai taken “Amana ta” da mawaki Hamisu Breaker ya rera, inda ta shawarci matasa da su guji sauraren wakar, bisa yadda take ɗauke da abubuwan da ke ƙarfafa aikata alfasha, da kuma amfani da kalmomin batsa a cikin bidiyon ta.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Published

on

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.

Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.

Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.

Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.

Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.

Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.

Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta:- Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Trending