Connect with us

Labarai

Ganduje ya ki amincewa da murabus din Kwamishinoni 3

Published

on

Gwamna jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ki amincewa da murabus din shugaban ma’aikatan sa, Ali Haruna Makoda da wasu kwamishinoni uku.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar, wanda ya rabawa.

Ganduje, ya ki amincewa da murabus din Nura Muhammed Dankade, Sanusi Said Kiru, da Dr. Aminu Tsanyawa, kwamishinonin kasafin kudi da tsare-tsare, ilimi da lafiya.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya umarce su da su ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Gwamnan, ya amince da murabus din wasu kwamishinonin sa guda bakwai, wato, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, Mataimakin gwamnan jihar Kano ya ajiye mukamin kwamishinan noma, Murtala Sule Garo, kwamishinan kananan hukumomi da al’adun gargajiya domin ya tsaya takara. dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar APC, Ibrahim Ahmad Karaye, kwamishinan al’adu da yawon bude ido wanda zai tsaya a matsayin mai wakiltar mazabar Karaye/Rogo da Mahmoud Muhammad Santsi, kwamishinan sufuri na jihar Kano domin neman kujerar dan majalisar tarayya na jam’iyyar APC a kananan hukumomin Gabasawa da Gezawa.

Sauran sun hada da Musa Iliyasu Kwankwaso, Kwamishinan Raya Karkara mai wakiltar mazabar Kura/Madobi/ Garunmallam, Kabiru Ado Lakwaya, Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Kano don neman kujerar APC Gwarzo da Kabo a Karamar Hukumar Kabo a Jam’iyyar APC.

Gwamnan ya gode musu bisa gudunmawar da suke baiwa jihar tare da yi musu fatan alheri.

Labarai

Rahoto: Dalibi ya kawo credit 9 a qualifying ya yi tsauri da yawa – Mai duba jarabawa

Published

on

Wani tsohon mai duba sakamakon jarabawar qualifying a jihar Kano ya ce, ana duba gazawar biyawa dalibai kudin jarabawar qualifying ne yayin fitar da sakamako, saboda haka akwai rashin adalci akan lallai sai dalibai sun kawo credit 9

Tsohon mai duba sakamakon jarabawar, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.

Muna da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Yadda hadarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2 a Lambu

Published

on

Wasu motoci babba da karama, sun yi taho mu gama akan titin garin Lambu da ke karamar hukumar Tofa a jihar Kano, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane biyu, daya kuma ya jikkata.

Wasu da al’amarin ya faru a gaban idanunsu, sun bayyanawa wakilin mu na ‘yan Zazu , Abubakar Sabo cewar, mai karamar motar ne ya yi a ran hannu, wanda ya janyo faruwar hadarin.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Babban Labari: Mun kama mota makare da kayan fashewa da bindugu da harsashi a Kano – Kiyawa

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sami nasarar cafke wata mota makare da wasu kayayyakin da ake hada abubuwan fashewa da kuma bindigu kirar AK47 .

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya ce, sun samu nasarar kama motar kirar Mercedez a unguwar Bubbugaje dake karamar hukumar Kumbotso.

A cewar Kiyawa sun sami rahoran sirri ne akan motar wadda suke zargin an kawo ta daga Jihar Jigawa zuwa Kano makare da irin kayayyakin da suke zargin da sune ake hada abubuwan fashewa domin aikata ta’addanci.

Sanarwar ta kuma ce bayan samun rahotan sirri na kara sowar motar zuwa Kano, jami’an tsaron Puff Adder suka yi wa mator kawanya, wanda hakan yasa mutanan ciki suka tsere suka bar motar a nan.

“Mun samu nasarar gano bindiga kirar AK47 guda biyu da kuma kananan bindigu biyu kirar Pistol tare da alburusai dubu daya da dari takwas”. In ji Kiyawa.

Continue Reading

Trending