Connect with us

Manyan Labarai

Ganduje ya taya Tinubu murnar zama dan takarar shugaban kasa

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, da na Legas Babajide Sanwo-Olu, sun taya Bola Ahmed Tinubu, murnar lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC.

Gwamnonin biyu sun ce, nasarar Tinubu, alamun nasara ce a zaben 2023.

A cewarsu, Tinubu ne ya fi dacewa da mulkin Najeriya, saboda kwarewarsa ta shekara da shekaru.

Sannan sun ya bi shugaba Buhari bisa rawar da ya taka wajen ganin an gudanar da taron da zaben cikin kwanciyar hankali. In ji BBC.

Manyan Labarai

Haihuwa a gida na janyo rasa rai – Dr. Hadiza Ashiru

Published

on

Ƙwararriyar likitar Yara da ke asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano Dakta Hadiza Ashiru, ta shawarci mata masu juna biyu cewar, da zarar sun fara jin alamun Naƙuda su rinƙa hanzarin zuwa Asibiti, domin a basu agajin gaggawa, don gujewa fuskantar matsala ga lafiyar su.

Dr. Hadiza Ashiru, ta bayyana hakan yayin zantawar ta da tashar Dala FM Kano, a ranar Laraba 14 ga watan Mayun 2025.

Ta ce abin takaici ne yadda mace mai juna biyu take shafe tsawon lokaci tana zuwa Awo, amma idan Haihuwa ta zo mata take ƙauracewa zuwa Asibiti, lamarin da ta ce idan haihuwar ta zo da kuskure ana iya rasa ran macen, ta sha wahala daga ƙarshe a tafi da ita Asibiti babu shiri.

“Duk da aikin mu na likitanci da muke yi a Asibiti, amma a haka mu ke shiga lungu da saƙo muna wayar da kan mata domin faɗakar da su illar cutar sankarar bakin mahaifa, wadda ke haifar da yawaitar mutuwar su a yayin haihuwa, “in ji Dr. Hadiza”.

Har ila yau, likitar ta kuma ce, idan matsala ta faru da macen ana shan wahala wajen shawo kan matsalar, a don haka mata masu juna biyu su rinƙa zuwa Asibiti, domin su Haihu a can, don su samu wani sauƙi.

Continue Reading

Manyan Labarai

Za ayi dokar da za ta tilastawa kamfanoni ɗaukar ma’aikata kashi 75 ƴan Kano – Gwamnati

Published

on

A ƙoƙarin ta na ƙara samarwa Matasa aikin yi, gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin yin dokar da za ta tilastawa kamfanoni masu zaman kansu ɗaukar kashi 75 cikin 100, na ma’aikata yan asalin jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa akan batun ne ma gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamitin da zai rinƙa kula da ɗaukar ma’aikata bisa ƙa’ida a jihar.

A lokacin da yake ƙarin bayani yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki ranar Laraba a Kano, shugaban kwamitin, Dakta Ibrahim Garba, ya ce za a miƙa daftarin dokar ga majalisar dokokin jihar da kuma gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, domin amincewa da dokar.

“Za’a ɗauki wannan mataki ne da nufin magance matsalar rashin aikin yi da kuma zaman kashe-wando tsakanin matasa a faɗin jihar Kano, “in ji shi”.

Kazalika, Garba ya bayyana cewa Gwamna Abba Yusuf, ya kafa kwamitin ne domin magance damuwar da ƴan jihar ke fuskanta dangane da yadda wasu kamfanoni masu zaman kansu suke ƙin ɗaukar ƴan asalin jihar aiki a kamfanonin su.

Continue Reading

Manyan Labarai

Hisba za ta fara kamen matan auren masu zaman Majalisa a Kano

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta ce za ta fara kamen matan auren da suke zaman majalisa a cikin unguwanni, domin daƙile matsalar da ake fuskanta tsakanin ma’aurata.

Mataimakin babban kwamandan hukumar Hisbah na jihar Kano Dakta Mujahideen Aminudden Abubakar, shi ke ya bayyana hakan a zanatawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano, a ranar Laraba.

Ya ce hukumar ta lura da yadda zaman majalisar da wasu daga cikin matan aure suke yi, ke haifar da gulmace-gulmace, da yawo a gari, da kuma ɓatawa wasu rayuwa ta hanyar koya musu neman Mata da sauran Laifuka.

“Za mu sanya ƙafar Wando ɗaya da dukkanin matan aure masu zaman majalisa a cikin unguwanni, bisa yadda hakan ya saɓawa doka; jami’an mu za su fara yawo a cikin daren kaya don ɗakile wannan matsalar”in ji shi”.

Dr. Mujahedden, ya kuma yi kira ga magidanta da su ƙara kula da shige da ficen matan su, don gujewa fuskantar matsala a zamantakewar auren su.

Continue Reading

Trending