Connect with us

Lafiya

Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna

Published

on

An gano wani gida da ake ginawa a Unguwar Damfami a karamar hukumar Kumbotso da ake zargin ana cusa takardaun Kur’ani da Alluna da rubutu.

Al’ummar yankin, sun yi korafi kan ba za su bari a ci gaba da irin wannan ginin a cikin yankin su, saboda haka suke kubutar da aka kawo musu dauki.

Wakilin mu na ‘yan Zazu, Abba Isah Muhammad, na dauke da cikakken rahoton saurari wannan.

Lafiya

Rahoto: Kada matashi ya bari a ba shi kudi ya sha kayan maye a lokacin zabe – Kwamared Mai Salati

Published

on

Wani matashi dan gwagwarmaya a jihar Kano, Kwamared Adamu Mai Salati Hausawa, ya ce, kada matashi ya bari a ba shi kudi ya sha kayan maye a lokacin zabe.

Kwamared Mai Salati, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Lafiya

Naira tiriliyan 2.565 tallafin man fetur ya lakume saboda haka zamu janye – Gwamnati

Published

on

Ministar kuɗi, kasafi da tsare-tsare, Hajiya Zainab Ahmed, ta ce, gwamnatin tarayya za ta daina biyan kuɗin tallafin man fetur a watan Yunin 2023.

Hajiya Zainab ta bayyana haka ne a lokacin taron manema labarai da ta gudanar a Abuja bayan kammala taron tattalin arziki na ƙasa karo na 28.

Kamfanin dillacin labarai na NAN ya ruwaito cewa, biyan tallafin kudin man fetur ya laƙume Naira tiriliyan 2.565 tsakanin watan Janairu zuwa Agustan 2022.

Haka kuma a cikin kasafin kudinta, gwamnatin tarayya ta ƙiyasta kashe naira tiriliyan 3.3 wajen biyan tallafin man tsakanin watan Janairu zuwa Yunin 2023.

Ta ci gaba da cewa kuɗin tallafin man na kawo wa kasafin kudin giɓin da dole sai an ciwo bashi kafin cike shi.

“Ba kuɗi ne da muke da su a hannu ba, kudi ne da muke karɓo bashinsu domin biyan tallafin”, A cewar Zainab.

Continue Reading

Lafiya

Rahoto: Aikin Hisba ba iya kalallahu kala rasulu ba ne kawai sai da horon kare kai – Ibn Sina

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta ce, aikin Hisba ba iya kalallahu kala rasulu ba ne kawai sai da horon kare kai

Babban kwamandan hukumar Hisbar, Sheikh Muhammad Harun Ibni Sina ne, ya bayyana hakan, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.

Akwai cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Trending