Addini
Rahoto: A yi addu’a a zaɓen 2023 domin samun shugabanni nagari – Aminu Khidir

Limamin masallacin Muniral Sagir da ke Eastern Bypass, malam Aminu Kidir Idris ya ce, al’umma su yi addu’a a zaben 2023, domin samun shugabanni nagari.
Malam Aminu Khidir ya bayyana hakan ne, yayin da yake yiwa gidan rediyon Dala karin bayani dangane da hudubar da ya gabatar.
Akwai cikakken bayanin hudubar a muryar da ke kasa.

Addini
Abubuwan da ya kamata mu yi a lokacin da muke cikin fushi.

- Fushi daga shaidan yake
- Mu yawaita zama da Alwala da kuma ambaton Allah
- Mu guji daukar hukunci lokacin da muke cikin fushi .
A shafin sa na facebook, Falalu Dorayi yayi tsokaci kan abubuwan dake jawo fushi, da kuma hanyoyi kauce musu kamar haka
Tasirin fushi a zucivar Dan Adam na iva haifar da masifu da abubuwa marasa dadi iri iri, ciki harda kisan kai.
Duk Lokacin da Dan Adam yake cikin fushi ko wani vanayi na bacin rai,Tabbas wannan mutumin na samun bakuncin Shaidan kusa da zuciyarsa, kuma duk hukuncin da zai yi a wannan lokacin ba zai zamo mai inganci ba,ma’ana zai dauki hukunci mara dadi.
Idan muka samu kanmu a irin wannan yanayin Ma’aiki Rasulullah (SAW) Ya bamu mafita:
- Mu daura Alwala
- Mu yawaita fadin “A’udhu billahi minashaytaan-ir-rajeem”
- Idan a tsaye muke mu zauna, idan bamu daina fushin ba kuma mu kwanta.
Kada mu biyewa zuciya, mu kasance masu hakuri.
Rahoto: Koyi da halayen Annabi ne nuna tsantsar kaunar sa – Limamin Tukuntawa
Ubangiji Yana son masu hadiye fushi da yafiya lokacin da aka fusata su.
Mu duba; (Ali Imran 3:134)
Allah Yasa mu dace

Addini
Rahoto: Gaɓoɓi shaida ne ga abinda mutum ya aikata ranar Alkiyama – Limamin Tukuntawa

Babban limamin masallacin Juma’a na Masjidul Quba dake unguwar Tukuntawa, Malam Ibrahim Abubakar Tofa, ya ce, akwai bukatar musulmi su yi kokarin aikata alkhairin, domin Gaɓoɓinsu, zasu bayar da shaidar duk abinda suka yi a ranar Alkiyama.
Malam Ibrahim Tofa, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.
Akwai cikakkiyar a hudubar a muryar da ke kasa.

Addini
Rahoto: Mu dauki aikin alheri wanda ba za mu daina yi ba – Limamin Tukuntawa

Limamin masallacin Juma’a na Masjidul Quba dake unguwar Tukuntawa, Mallam Ibrahim Abubakar Tofa, ya ce, akwai bukatar mutum ya dauko aikin alheri wanda zai ci gaba yi ba tare da ya daina ba.
Mallam Ibrahim Tofa, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.
Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano