Addini
Rahoto: Maniyyata sun yi zanga-zanga a Kano

Maniyya sama da dari biyu sun gudanar da zanga-zangar lumana a jihar Kano, dangane da zargin hukumar jin dadin Alhazai ta jihar ta ki ba su kujerun su bayan kudadensu da suka yi tuntuni kamar yadda aka tsara.
Sai dai sakataren hukumar jindadin Alhazai na jihar kano Muhammad Abba Danbatta yace suna tsaka da shawo kan korafin da maniyyatan suka yi domin samo musu mafita.
Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.
Addini
Rahoto: A rinƙa kyautata alwala yadda Manzon Allah (S.A.W) ya yi – Limamin Al-Muntada

Limamin masallacin Juma’a na Almundata da ke unguwar Dorayi, a karamar hukumar Gwale, jihar Kano, malam Nura Sani, ya ce, al’umma su rinka kyautata alwala, domin tana daga cikin manyan ibadu da Allah ya shar’anta ga bayinSa.
Malam Nura Sani, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Abba Isah Muhammad, yayin da yake karin bayani, dangane da abinda hudubar da ya gabatar ta kunsa.
Muna da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.
Addini
Rahoto: Mu rinƙa ƙoƙarin zuwa sallar Juma’a a kan lokaci – Limamin hukumar sharia

Limamin masallacin Juma’a na hukumar shari’a ta jihar Kano, Dayyib Haruna Rashid, ya ce, akwai buƙatar al’ummar musulmi, su rinƙa zuwa masallacin Juma’a a kan lokaci.
Malam Dayyib Haruna Rashid, ya bayyana hakan a zantwarsa da walikin mu na ƴan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Ɗinki.
Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.
Addini
Rahoto: Azumin Tasu’a da Ashura na kankare zunuban shekara guda – Limamin Tukuntawa

Limamin masallacin Juma’a Na Masjidul Ƙuba da ke unguwar Tukunwa, Malam Ibrahim Abubakar Tofa, ya ce, Azumin Tasu’a day Ashura Na kankare zunuban shekara guda.
Malam Abubakar Tofa, ya bayyana hakan ne, a zantwarsa da walikin mu Na ƴan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Ɗinki.
Akwai cikakken rahoton a muryar da ke ƙasa.
-
Nishadi3 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai2 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Lafiya2 months ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano