Connect with us

Manta Sabo

Badala: Kotu ta daure mawakin Amurka R.Kelly na tsawon shekaru 30

Published

on

An yanke wa mawakin R&B, R. Kelly, hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari a ranar Laraba.

Hakan ya biyo bayan hukuncin da aka yanke masa ne a shekarar da ta gabata kan laifin yin lalata. Ana zargin Kelly da yin amfani da sunansa wajen kama wadanda ya yi lalata da su cikin tarko.

Masu gabatar da kara sun bukaci alkalin da ya yanke wa dan shekaru 55 hukuncin daurin shekaru sama da 25 a gidan yari, yayin da lauyoyin da ke kare shi suka nemi a ba su 10 ko kasa da haka, suna masu cewa bukatar masu gabatar da kara ta kasance “daidai da hukuncin daurin rai da rai.

A watan Satumban da ya gabata, wata alkali ta yankewa Kelly laifi kan tuhume-tuhume tara, da suka hada da cin hanci da rashawa da kuma laifuka takwas na keta dokar, dokar safarar jima’i.

Masu gabatar da kara daga Gundumar Gabashin New York sun zargi Kelly da yin amfani da matsayinsa na shahararre da kuma “cibiyar sadarwar mutanen da ke hannun sa wajen kai hari ga ‘yan mata, maza da mata don jin dadin jima’i.

Manta Sabo

Raini: Kotu ta yi watsi da hukuncin da aka yi wa Shugaban EFCC

Published

on

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da hukuncin da ya shafi shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa da laifin raina kotu.

Mai shari’a Chizoba Oji ce ta ya yi watsi da hukuncin a ranar Alhamis, bayan sauraron ƙorafin da shugaban hukumar yaƙi da rashawa da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati ya shigar.

Kotun ta ce ta gano cewar ba za a iya cewa shugaban na EFCC ya raina kotu a lokacin da aka yanke hukuncin ba, kasancewar ya riga ya bayar da umurnin a mayar wa wanda ya shigar da ƙarar motarsa ƙirar Range Rover.

Kotun ta ce takardu sun nuna cewa an fara shirin mayar wa mai ƙorafin motarsa da kuma kuɗi naira miliyan 40.

A ranar Talata ne mai shari’a Chizoba Oji ta yanke hukuncin cewar EFCC ta raina kotu ta hanyar ƙin bin umurnin hukuncin da ya ce a mayar wa wani mutum motarsa da kuma kuɗi naira miliyan 40.

Continue Reading

Manta Sabo

Za a fara sauraron shaidu a kan zargin kisan da Dan China ya yi a Kano

Published

on

Babbar kotun jihar Kano mai zaman ta a Miller Road karkashin jagorancin mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji, ta sanya ranan 16 da 17 da kuma 18 ga watan gobe wato Nuwamba, domin fara sauraron shaidu a kunshin tuhumar da gwamnati ta ke yi wa dan kasar China Mr. Frank wanda a ke zargin ya kashe wata matashiya a Kano.

A zaman kotun na yau an gabatar da wani mutum mai suna Mr. Gao Cumru a matsayin wanda zai fassara yaren turanci zuwa yaren mandarin na kasar China.

Kuma an karanta tuhumar nan take laifin da ake zargin dan Chinan ya saba da sashi na 221 na kundin penal code sai dai ya musanta zargin nan take.

Kwamishinan shari’a Barrister Musa Abdullahi ya bayyana cewar za su gabatar da shaidu.

Bayan fitowa daga kotun kwamishinan ya bayyana cewar, cikin wata 2 suke sa ran kammala shari’ar

Shi ma lauya dan China barrister Yusuf Abdullahi ya bayyana matsayar su a kan shari’ar

Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewar ranakun 16, 17 da 18 ga watan gobe sune za a saurari shaidun masu kara

Continue Reading

Labarai

Kotu ta wanke Saminu Turaki daga tuhumar EFCC

Published

on

Babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Dutsen jihar Jigawa, ta wanke tsohon gwamnan jihar, Saminu Turaki daga tuhumar da hukumar EFCC ke yi masa na almundahana da kuɗi Naira biliyan 8.3.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ce ta kai tsohon gwamnan da wasu kamfanoni uku, ƙara tun a shekara ta 2007 kan laifuka 33 da a ke tuhumar su.

Alƙalin da ya yanke hukunci, mai shari’a Hassan Dikko, ya yi watsi da dukkanin tuhume-tuhume da ake wa tsohon gwamnan, bisa hujjar rashin mayar da hankali daga ɓangaren waɗanda suka shigar da ƙara.

Kotun ta umurci a mayar wa Saminu Turaki takardunsa na tafiye-tafiye.

Continue Reading

Trending