Connect with us

Manta Sabo

Wani dan Najeriya mazaunin Uganda ya shiga hannu bisa zargin satar wayoyin mutane

Published

on

‘Yan sanda a garin Fort Portal na kasar Uganda sun cafke wani dan Najeriya mai suna, Musa Oze, bisa zargin satar wayoyin hannu.

An kama Oze kuma an tuhume shi da Patrick Tumusiime, Bob Amanyire, da Mugenyi Hamidu dukkansu mazauna Fort Portal dake kasar Uganda.

Kamen nasu ya biyo bayan daya daga cikin wadanda aka sace wa wayar ta kai rahoto ga ‘yan sanda. Vincent Twesigye mai magana da yawun ‘yan sandan yankin Rwenzori ya ce ‘yan sandan sun yi amfani da kyamarori na CCTV kuma sun sami damar bin diddigin Tumusiime.

A cewar Twesigye, a lokacin da ake yi wa Tumusiime tambayoyi, ya jagoranci ‘yan sanda zuwa Amanyire, wani makanikin waya a Fort Portal wanda kuma ke sayar da wayoyi na hannu.

A nan ne ‘yan sanda suka gano Oze, wanda a cewar binciken ‘yan sandan, shi ne ke da hannu wajen karkatar da lambobin wayoyin da aka sace. A cewar ‘yan sanda, Amanyire ya gaza yin lissafin hannun jarin da ya kai har aka kama shi.

Rundunar ‘yan sandan ta ce tana kuma binciken yadda Oze ya shigo kasar da kuma yadda ya fara mu’amala da wayoyin hannu.

Rundunar ‘yan sandan ta lura cewa wasu daga cikin wadanda abin ya shafa da barayi suka rasa wayoyi suna sha’awar sauya Sim Card dinsu ne kawai ba tare da kai rahoton sata ga ‘yan sanda ba wanda ya ce yana kawo cikas ga bincike.

Manta Sabo

Kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar Alhaji Alhassan Aminu Ɗan Tata, ta tabbatar wa iyalan Sharu Ilu Rami a Kano

Published

on

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a sakatariyar Audu Baƙo a jihar Kano, ta yi hukunci akan shari’ar da dattijon nan Alhaji Alhassan Aminu Ɗan Tata ya ɗaukaka, akan wani babban rami da aka yi taƙaddama akansa da ke unguwar Gwammaja a jihar.

Tunda fari dai dattijon ya ɗaukaka ƙarar ne akan hukuncin da babbar kotun kotun jaha ƙarkashin mai Shari’a Justice Usman Na Abba, ta yi, inda ta mallaka wa iyalan marigayi Sharu Ilu ramin, lamarin da dattijon ya ɗaukaka ƙarar.

Sai dai kuma a zaman kotun na yau Laraba, alkalin da ya jagoranci yanke hukuncin a kotun ɗaukaka ƙarar Justice U-A Musalli, ya kori ƙarar dattijon, tare kuma da tabbatar da hukuncin kotun ƙasa, ma’ana dai a baiwa magada iyalan marigayi Sharu Ilu ramin kamar yadda aka yi hukuncin baya a kotun ƙasan.

Bayan fitowa daga kotun ne wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u, ya yi duk mai yiyuwa dan ji daga ɓangaren lauyar Dattijo Alhaji Alhassan Aminu Ɗan Tata, mai suna Veronika, sai dai ta ce ba abinda za ta ce, a nan ne ya wai-wayi guda daga cikin lauyoyin waɗanda akayi ƙara mai suna Yahya Y Sharif, wanda ya ce daman haka suka yi tsammani, kuma gashi gaskiya tayi halin ta.

Daga bisani dai kotun ta ce a shirye take da ta baiwa kowanne bangare kwafin hukuncin, kuma duk wanda bai gamsu da hukuncin ba yana da dama ya wuce kotun gaba.

Aƙalla dai an shafe sama da shekaru biyar ana taƙaddamar ramin dake unguwar Gwammaja a Kano.

Continue Reading

Manta Sabo

Kotu ta aike da ƴan Daudu 5 gidan yari kan zargin kai hari ofishin Hisbah a Kano.

Published

on

Babbar kotun shari’ar muslunci dake zamanta a shahuci ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Muhammad Sani Ibrahim, ta aike da wasu matasa 5 gidan gyaran hali zuwa ranar 15 ga watan gobe.

Tun da fari gwamnatin jahar kano ce ta gurfanar da su bisa zargin sun haɗa baki da yin wasan Bori, ɓarna da kuma lalata kayan gwamnati.

Kunshin tuhumar ya bayyana cewar matasan sun haɗa baki sun kai farmaki ofishin Hisbah dake unguwar Bachirawa ƙarshen kwalta, inda suka ragargaje motar hukumar Hisbar yankin suka kuma farfasa gilashin tagar ofishin Hisbar.

Matasan sun hadar da Nasiru Hamisu, da Aminu Sani, da kuma Auwal Haruna, sai Auwal Tasi’u sai kuma Musa Umar.

Yayin da aka karanta musu tuhumar a gaban kotun matasan sun musanta, lauyansu Barister Aliyu Bashir Buba ya roki kotun da ta sanya su a hannun beli, sai dai kuma lauyan gwamnati Barister Zaharaddin Mustafa ya yi suka.

Lauyan gwamnati ya bayyana cewar kotu uwar kowa ce, kuma yana tsoron kada a bayar da belin wani abu ya biyo baya tunda matasan sun tunzura mutanen unguwar Bachirawar Tukwane.

A nan ne kotun ta aike da matasan su biyar gidan gyaran hali zuwa ranar 15 ga watan gobe.

Wakiliu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewar laifukan da ake tuhumar matasan sun saɓa da sashi na121, da na 277 da kuma na 364, sai kuma sashi na 386 na kundin Penal code.

Continue Reading

Manta Sabo

Kotu ta yi umarnin a binciki lafiyar kwakwalwar Hafsat Cucu karo na biyu

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 31 ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Zuwaira Yusuf, ta yi umarnin da a yi wa Hafsat Cucu gwajin kwakwalwa dan a gano ko tana da cikakken hankali.

A zaman kotun na yau mai shari’a Zuwaira Yusuf, ta kuma bayyana cewar masu gabatar da kara sun kawo shaidu a tuhumar da suke yiwa wasu mutane 3, da suka haɗar da mijin Hafsat Ɗayyabu Abudullahi da Adamu Muhammad da kuma Nasidi Muhammad.

Ana zargin waɗannan mutane da laifin haɗa baki da boyewa hukuma bayani, yayin da ita kuma Hafsat ake zarginta da laifin kisan kai.

Kunshin zargin da ake yiwa Hafsat ya bayyana cewar tun a ranar 21 ga watan 12 na shekarar 2023, ne Hafsat ta hallaka wani mai suna Nafi’u ta hanyar daɓa masa wuka har ya rasu.

An kuma zargi mijinta da waɗannan mutane da laifin boyewa hukuma jawabin faruwar lamarin.

A zaman kotun na baya kotun tayi umarnin da a binciki kwakwalwar Hafsat cucu kuma a yau an gabatar da sakamakon binciken, sai dai kotun bata karanta shi ba ta kuma yi umarnin a je a sake auna kwakwalwar a karo na biyu.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewar, kotun ta sanya ranar 26 ga watan gobe dan fara sauraron shaidu.

Continue Reading

Trending